Rikicin Somalia
November 2, 2006Gwamnatin riƙwan ƙwarya, a Somalia, ta yi wastsi da sabuwar shawara komawa tebrin tantanawa, da dakarun kotunan islama.
Kakakin gwamnatin, Ahmed Omar Gagale, ya rataya lefin cijewar tantanawar, a kan shugabanin kotunan Islama.
Kamar yadda ƙila, ku ka riga kuka sani, jiya ne, a ka watse baram-baram, tsakanin tawagogin 2, a taron sulhun da su ka shirya, birnin Khartum na ƙasar Sudan, bisa jagoranci ƙungiyar haɗin kan ƙasashen larabawa.
Jim kaɗan bayan wargajewar wannan taro, ministan harakokin wajen Somalia, Isma´ila Hourre Bouba, ya ce gwamnatin riƙwan ƙwarya, ta daina ɗaukar dakarun Kotunan Islama, a matsayin abokan tantanawa.
Hanya mafi dacewa da ta rage yanzu,itace kawai ɓarin wuta tsakanin ɓangarorin 2,kuma jiki magayi.
A halin da ake ciki, ɓangarorin 2, su nja daga, cikin shirin ta kwana.