1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jagoran 'yan adawa na Venezuela ya bukaci goyon bayan sojoji

Suleiman Babayo MAB
April 30, 2019

An samu boren wasu sojojin Venezuela da gwamnati ta murkushe yayin da 'yan adawa ke kara kaimin neman kawo karshen gwamnatin kasar karkashin Shugaba Nicolas Maduro.

https://p.dw.com/p/3Hijh
Venezuela Kampf um Militärbasis  La Carlota
Hoto: picture-alliance/dpa/R. Hernandez

Jagoran 'yan adawa na Venezuela Juan Guaido ya fantsama kan titi tare da wasu 'yan gwagwarmaya tare da neman sojoji su taimaka wajen kawo karshen gwamnatin Shugaba Nicolas Maduro, abin da ke kara tabarbara rikicin siyasa a kasar da ke yankin Latin Amirka. Shi dai jagoran 'yan adawa Guaido ya bayyana a wajen gangamin tare da dan-gwagwarmaya Leopoldo Lopez wanda ya yi ikirarin jami'an tsaro da suka karbi umurnin jagoran 'yan adawa suka sako shi daga kamun da gwamnatin ta yi masa. Ministan tsaro Vladimir Padrino ya bayyana murkushe boren wasu sojoji.

Tuni gwamnatin kasar Spain ta bukaci ganin gudanar da zabe cikin lumana domin kauce samun tashe-tahsen hankula a zubar da jini a kasar ta Venezuela, inda Firamnista Pedro Sanchez na Spain ya tabbatar da cewa yana saka ido kan lamuran da suke faruwa a kasar ta Venezuela.