Rikicin Siyasar Bangladesh ya yi ƙamari | Labarai | DW | 09.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Siyasar Bangladesh ya yi ƙamari

A ƙasar Bangladesh 'yan adawa na fuskantar barazana daga ɓangaren gwamnati wacce ke naman murƙushesu da ƙarfin tuwo.

Hukumomi a ƙasar ta Bangladesh sun cafke shugabannin babbar jam'iyyar adawar ƙasar su guda uku gabannin babban zaɓen ƙasar da za a gudanar a shekara mai zuwa.

Jami'an 'yan sanda sun cafke Moudud Ahmed da M.K Anwar da kuma Rafiqul Islam Mia na jam'iyyar adawar a jiya Jumma'a, sa'oi ƙalilan bayan da haɗakar ma'aikatan ƙungiyar ƙwadago ƙarkashin jagorancin jam'iyyar adawa ta Bangladesh Nationalist Party, suka sanar da fara yajin aikin a gobe Lahadi. Rahotanni sun bayyana cewar yajin aikin na kwanaki uku, an shirya yin sa ne domin tilastawa Firaministan ƙasar Sheikh Hasina sauka daga kan karagar mulki tare da naɗa wani shugaban na wucin gadi da zai lura da al'amuran zaɓen da za a gudanar a ƙasar.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Abdorahamane Hassane