Rikicin siyasa na ruruwa a Guinea | Labarai | DW | 24.09.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin siyasa na ruruwa a Guinea

Jagoran 'yan adawa na kasar Guinea ya yi gargadin samun rikici na kabilanci bayan wasu kalaman Shugaban kasar.

Jagoran 'yan adawa na kasar Guinea Conakry, Cellou Dalein Diallo ya zargi Shugaba Alpha Conde da neman tayar da rikici tsakanin kabilun kasar, abin da ka iya jefa kasar kasadar fadawa a yakin basasa. Kamalan jagoran 'yan adawa sun biyo bayan wata sanarwa ta fadar shugaban kasa da ke neman goyon baya na kabilanci gabanin zaben watan Oktoba.

Shugaba Conde dan shekaru 82 da haihuwa ya yi gyara ga kundin tsarin mulkin kasar domin samun wa'adi na uku na mulki, lamarin da ya jefa kasar cikin rudanin siyasa.