Rikicin siyasa a Siri Lanka | Labarai | DW | 11.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin siyasa a Siri Lanka

Kotun kolin Siri Lanka ta amince wa shugaban kasar samun tazarce a wa'adi na uku

Kotun kolin kasar Siri Lanka ta yanke hukuncin cewa shugaban kasar na iya yin tazarci a wadadi na uku. A cewar kotun kolin kasar Shugaba Mahinda Rajapaksa, babu wata ayar dokar kasar da ta hana shugaban sake tsayawa takara.

Kasar Siri Lanka ta yi suna wajen take 'yancin dan Adam, ga kuma bala'in talauci da ya addabi 'yan kasar. Yanzu haka kungiyoyin kare 'yancin dan Adam na duniya na tuhumar shugaban kasar da aikata kisan kiyashi kan 'yan kabilar Tamil, a lokacin da gwamnatin kasar ta yi amfani da karfi wajen murgushe 'yan tawayen Tamil Tigers.

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Suleiman Babayo