Rikicin siyasa a Jamhuriyar Nijar | Siyasa | DW | 16.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rikicin siyasa a Jamhuriyar Nijar

Shekaru 22 da fara mulkin dimokaradiyya a Jamhuriyar Nijar, masu fashin baki na ganin har yanzu tsoffin hannu ne suka mamaye harkokin siyasar kasar.

A Jamhuriyar Nijar a daidai lokacin da ce-ce-kucen siyasa ke ci gaba da yin kamari, wasu masu nazarin al'amuran siyasar kasar na ganin lokaci ya yi da ya kamata a samu canjin shugabannin siyasa, domin kuwa a ganinsu tsofaffin 'yan siyasar da suka mulki kasar tun bayan komawa kan turbar dimokaradiyya a tsahon shekaru 22 da suka gabata sun nuna gazawa musamman wajen kasa fitar da kasar daga kangin talauci da matsalolin rayuwa na yau da kullum sakamakon abin da suka bayyana da son kai da rashin kishin kasa. Ko da ya ke wasu tsofaffin 'yan siyasar na musanta wanann batu.

Tun dai bayan da kasar Nijar ta koma kan turbar mulkin dimokaradiyya manyan shugabannin siyasa biyar zuwa shida wadanda suka fito daga manyan jamiyyun siyasa uku zuwa hudu na kasar ta Nijar ne kawai ke yin rawar 'yan mata a kan kujerar mulkin kasar. To saidai wasu masu lura da tafiyar al'amurran siyasar kasar, na ganin lokaci ya yi na ta canza zani domin kuwa wadannan shugabannin siyasa sun kawo makurar fasaharsu ba tare da dora kasar ta Nijar a kan turbar ci gaba ba. Hasalima sune sanadiyyar koma bayan da take fuskanta duk da arzikin da Allah ya huwace mata.

Brunnen in Zentral-Niger (Zinder)

Makiyaya a Zinder na neman ruwan sha.

Malam Nasiru Seidu shugaban kungiyar garar hula ta Muryar Talaka na daga cikin masu irin wannan ra'ayi in da ya ce..

"To matsalar tamu ta kasarmu mine ne , tsofin 'yan siyasa sun yi katutu ga wuri ba su shirya kowa ba karkashinsu an hana ka taso. Kana gani karara dan siyasa zai daurewa karya gindi, su yi dubara su gamu ta ko wanne fannin su hade su samo iko tsakankaninsu. Sun san yadda za su yi dubara su tahi da shi koda ikon baya gyara talakka, su ba shine a mahimmacin garesu ba, hadamar dukiyoyin kasa da ake yi har yanzu an gaza kokowa da shi saboda 'yan siyasa sun gama kansu guri guda sun kiya, dan haka yanzu Nijar a kwai 'yan siyasa wadanda kwata-kwata ya kmata a ce an janye su daga siyasa saboda ba siyasar ci gaban kasa su ke yi ba, har juyin milki da ake yi a Nijar mutane na cewa halin' yan siyasa ne".

Sai dai ga dukkan alamu ba kungiyoyin farar hulane kadai ke da irin wanann tunani a kan 'yan siyasar kasar ta Nijar ba. Honnorable Ben Omar Mouhamed shahararren dan siyasa ne a Nijar, amma kuma ya ce biri ya yi kama da mutun kan wannan batu.

"Jam'iyyun nan da shugabanninsu suka je Conference Nationale, in ka duba yau yawanci sune wadanda su ka yi ruwa su ka yi tsaki tun daga 1991 zuwa yau. Kuma duk wanda ya ce zai yi takara da su ya ja wa kansa jaraba, sai ta zamanto kawai wata sarauta ce ta gargajiya, tawa ce da ni da Iyalina da yan uwana, in ka na so ka zauna in ba ka so ka tafi, kuma duk wan da ya ce zai kawo wani sauye-sauye za a nemo hanyoyin da za a tsige shi dan masu hana ruwa gudu ne".

Mahamane Ousmane 1995 Präsident Niger

Zababben shugaban farar hula na farko a Jamhuriyar Nijar Mahamane Osman.

To amma da yake mayar da martani a kan wannan zargi da wasu ke yiwa rukunin 'yan siyasar kasar ta Nijar na yau da ake yiwa kallon wadanda su ka ci na jiya su ka ci na yau, su ka ci nasu su ka ci na maras ci, mai ci su ka ci tare da shi, shahararren dan siyasar nan Alhaji Sanusi Tambari Jaku shugaban jamiyyar PNA Al'umma, cewa ya yi zargin da ake yi musu ba shi da tushe ballantana makama.

"Shin wai su mutanan ga masu cewa 'yan siyasa sun yi rawarsu an gani sun lalata kasa su ba sabon jini to su me su ka gyara? Ko su basu da laifi ne? To su shafawa mutane lafiya domin mutane ne cikin rayukansu akwai kyashi, shin wai wadan ne 'yan siyasa ne ma suka kasa? Mahammane Usmane ya kasa ne? Mahammadu Isuhu ya kasa ne? Sanusi Jaku ya kasa ne? Hamidu Algabid ya yi zama har Firaminista a lokacin nan ba a ce bai san komi ba ya kasa, sai yanzu? Su wadannan da suke cewa mun kasa wasu ma a cikin su mu muka karantasshe su, to in kana son ka zamo shugaban jamiyya ta siyasa babu wanda ya hana ka da ka tashi can kana korahin wani tsoho y rike wuri, tahi can kaima ka share gurinka".

Wasu dai na ganin in bera na da sata to daddawa ma na da wari, domin kuwa a dai dai lokacin da ake zargin tsofaffin 'yan siyasar da yin kaka gida akan harkokin mulki, halin kwadayi na sanyawa akasarin matasan da ake sa ran za su iya maye gurbin tsofaffin 'yan siyasar ci gaba da kasancewa 'yan amshin shatar shugabanni.

Mawallafi: Gazali abdu Tasawa
Edita: Lateefa Mustapha Ja'afar/ ZMA

Sauti da bidiyo akan labarin