Rikicin siyasa a Afirka ta Kudu | Labarai | DW | 05.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin siyasa a Afirka ta Kudu

A karon farko tsofaffin shugabannin Afirka ta Kudu sun bukaci taron kasa na masu fada aji, da nufin daukar matakan gaggawa na kawo karshen rikicin siyasa da ke haifar da rudani a fadin kasar.

Südafrika Präsident Jacob Zuma (Getty Images/AFP/R. Jantilal)

Shugaban Afirka ta Kudu, Jacob Zuma.

A baya-bayannan dai an gudanar da zanga-zanga mai tarin yawa, inda jam'iyyar adawa ke kira ga shugaba Jacob Zuma ya sauka daga mukaminsa. Tsofaffin shugabannin da suka yi nazarin sulhunta rikicin siyasar kasar, sun hada da Thabo Mbeki da Frederik Willem de Klerk da Kgalema Montlanthe da kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Phumzile Mlambo-Ncuka. Tsofaffin shugabannin dai sun yi gargadi kan halin rashin tabbas da rikicin siyasa ka iya jefa kasar ciki, musamman ta fannin tattalin arziki wanda kuma ka iya zama bulaliyar kan titi. 

Shugaba Zuma dai na fuskantar zarge-zargen cin hanci da karkatar da lalitar gwamnati da ma zargin tube wasu mukarraban gwamnati ba bisa ka'ida ba, inda a baya-bayannan ya sauke ministan kudin kasar daga mukaminsa. Yanzu dai shugaban na fuskantar matsin lamba daga jagororin jam'iyarsa ta ANC wandaya ya sa wata kotu ta umarci Zuma da gabatar da kwararan hujjoji na garambawul da yake kokarin yi a kasar.