Rikicin Siriya na bazuwa ga maƙobta
November 12, 2012Jiragen yaƙin gwamnatin Siriya sun tsaurara hare-hare kan ma buyar yan tawaye dake iyakar ƙasar da ƙasashen Turkiya da Isra'ila. Wani harin da dakarun gwamnatin Siriya suka kai a kan mafakar yan tawaye a kusa da iyakarsu da Turkiya, ta firgeta jama'a da yawa, inda a can kan iyakarsu da Isra'ila, nan ma Siriya ta cilla makamai kan inda yan tawaye suka kafa sansani. Ko da a ranar lahdi ma, sanda wata rokar da Siriya ta cilla ya shiga cikin yakin tuddan Golan wanda Isar'ila ta mamaye tun yaƙin shekara 1973, abinda ma ya sa a karo na farko Isra'ilan ta yi harbin gargadi cikin Siriya. Sakatare janar na MDD Ban Ki-moon ya bayyana damuwa kan yadda yaƙin na Siriya ke ƙara bazuwa, inda ya yi ƙira da a mai da suciya nesa. Yan tawayen Siriya da suka yi sansani a kusa da tuddan Golan sun yi ƙazamin karawa da sojan gwamnatin Siriya a ranar Lahdin da ya gabata. Shi kuwa magajin garin Cailapinar dake iyaka da Siriya ta ƙasar Turkiya, yace bama baman da jiragen yaƙin Siriya suka cilla, ya hallaka mutane aƙalla 20 yayin da wasu da dama suka jikkata.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Yahouza Sadissou Madobi