Rikicin sakamakon kisan wani matashi a Amirka | Labarai | DW | 20.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin sakamakon kisan wani matashi a Amirka

Kisan wani matashin baƙar fata na ci gaba da janyo tashin hankali a Jihar Missouri ta Amirka

Babban mai gabatar da ƙara na Amirka Eric Holder zai kai ziyara a wannan Laraba zuwa garin Ferguson na Jihar Missouri, inda aka kwashe kwanaki ana artabu da masu zanga-zanga kan kisan wani matashi baƙar fata da wani ɗan sanda ya yi, abin da ya haifar da mahawara kan yadda ake mu'ammala da tsiraru.

Holder zai jagoranci tawagar gwamnati kan lamarin na kisan Michael Brown ɗan shekaru 18 da haihuwa da duba yiwuwar amfani da ƙarfi ta hanyar da ta saɓa doka, inda tuni aka kama mutane 47 masu zanga-zanga. Tuni aka tura dakaru domin tabbatar da doka da oda a yankin, yayin da Shugaba Barack Obama ya ce 'yan sanda ba su da wata hujja ta amfani da ƙarfin da ya wuce kima.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Abdourahamane Hassane