1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin PDP a Najeriya na ƙara fitowa fili

August 30, 2013

Rigingimu na ƙara dabaibaye jam'iyyar PDP mai mulki a Najeriya biyo bayan ƙaurace wa babban taron jam'iyyar da wasu wakilai suka yi.

https://p.dw.com/p/19ZHY
Nigerian President Goodluck Jonathan speaks during a nationwide live broadcast on the state television on May 14, 2013. President Goodluck Jonathan has declared state of emergency in the nation's troubled northeast states of Yobe, Borno and Adamawa, where Islamic extremists now control some of the country's villages and towns, promising to send more troops to fight what is now an open rebellion. AFPPHOTO/PIUS UTOMI EKPEI (Photo credit should read PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images)
Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Gira-gizon rigingimun da suke ci gaba da luluɓe jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriyar dai na ƙara yin duhu saboda yadda lamarin ke ƙara faɗaɗa kama daga rikicin da wutarsa ta daɗe tana ruruwa a matakin ƙasa na jam'iyyar har zuwa ga jihar Anambra inda jam'iyyar ta kai ga dakatar da Andy da Chris Ubah bisa laifin gudanar da haramtaccen zaɓen fidda gwani, inda aka sanar da Andy a matsayin ɗan takara neman gwamnan jihar.

Manya ƙalubale da ke a gaban jam'iyyar ta PDP

Zancen duka ɗaya ne a jihar Rivers inda kallon hadarin kajin da ke ci gaba da faruwa tsakanin gwamnan jihar Rotimi Amaechi da uwar jam'iyyar har ma da fadar shugaban Najeriya ya sanya shi ɗaukacin wakilan jihar kama hanyar ƙaurace wa babban taron da za'a gudanar a wannan Asabar, ga kuma na baya-baya nan na jihar Taraba da jam'iyyar ta gaza ɗaukan mataki a kai. Wannan ya sanya Hon Tuku El Sudi bayyana cewa lamari ne da ke tada hankali.

Nigeria Tag der Demokratie (29.05.2013): Nigerias Präsident Goodluck Jonathan und Namadi Sambo, sein Vize-Präsident; Copyright: DW/U. Musa
Hoto: DW/U. Musa

Babban taron jamiyyar ta PDP da ke zama wanda ya fi kowane rikici a tarihin kafuwar jam'iyyar da ma kame madafan ikon Najeriya da fiye da shukaru 14, domin kuwa har yanzu babu tabbas a kan ko za'a gudanar da zaɓen wanda zai cike gurbin muƙamin sakatren jam'iyyar da ake ci gaba da taƙaddama a kansa. Illar da wannan rigingimu ke yi ga jamiyyar da ma demokraɗiyya Najeriya na zama abin da ke ci gaba da ɗaga hankalin masoya ganin demokradiyya Najeriyar ta miƙe sambal, maimakon tafiya a karkace. To sai dai ga Malam Abubakar Umar Kari masanin zamankatkewa da kimiyyar siyasa da ke jami'ar Abuja ya ce

jamiyyar ta bar jaki ne kawai tana dukan taiki a yanayin da ka iya zama na a fasa kowa ya rasa.

Rashin tabbas akan gudanar da zaɓen na PDP

Ganin irin barakar da jam'iyyar PDP ke ciki musamman jan dagar da wasu gwamnoni shida suka yi a game da yiwuwar bai wa shugaban Najeriya damar tsaya takara ba tare da hamayya ba, da kuma ja da suke ƙara nunawa a kan jagorancin shugaban jam'iyyar Alhaji Bamanga Tukur wanda duk da ganawar da wasu suka yi da shi har yanzu babu wani sauyi na zama abinda ke daga hankalin wasu yayyan jamiyyar. Amma Aliyu Abubakar Tafidan Bodinga jigo a ƙungiyar tabbatar da mulki bisa adalci ya ce bai ga abin damuwa ba.

Wahlplakat von Dr. Bamanga Tukur, Präsident der PDP ,( Partei an der Macht in Nigeria) Foto: Ubale Musa, Haussa / DW
Hoto: DW/U.Haussa

A yayinda wata kotu a Abuja ta ummurci jam'iyyar ta janye korar da ta yiwa Andy da Chris Ubah abin jira a gani shi ne yadda za ta kaya a babban taron jam'iyyar da ya zo a dai dai lokacin da 'yan siyasar Najeriyar musamman cikin wani hali rashin tabbas.

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto haɗe da rahoton shirye-shiryen taron da wakilinmu na Abuja Ubale Musa ya aiko mana. Da kuma hira da Halima Balaraba Abbas ta yi da dokto B.B.Faruk malamin koyar da kimiyyar siyasa da kuma tattalin arziki a Jami'ar Abuja

Mawallafi : Uwais Abubakar Idris
Edita : Abdourahamane Hassane

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani