Rikicin Palasdinawa | Labarai | DW | 22.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Palasdinawa

Wasu yan bindiga dadi sun sace tsohon ministan sharia, arusasshiyar gwamnatin yankin palasdinawa da yan Hamas keda rinjaye,wadanda kuma suka rike madafan iko na tsawon shekara guda,a birnin Nablus dake gabar yamma da kogin Jordan.

Yan bindigan wadanda fuskokinsu ke rufe,sun cafke Ahmed al-Khaldi ,ne adaidai lokacin da yake barin masallaci,bayanj sallar jumaa a yau.Sace wannan ministan na hamas dai na mai zama martani na baya bayan nan akan kungiyar ta Hamas,bayan kwace madafan iko da tayi a zirin Gaza a makon daya gabata.

A yau din ne kuma wani babban commandan rundunar kungiyar Fatah ta shugaba Abbas,yayi murabus daga mukaminsa,sakamakon gazawansu wajen sake karbe madafan iko daga kungiyar ta hamas a Gaza.