Rikicin Masar ya ɗau sabon salo
July 25, 2013Talla
Sojoji a ƙasar Masar sun baiwa ƙungiyar Muslim Brotherhood kwanaki biyu da su shiga shirin gwamnati ko kuma su gamu da fushin hukuma. Wani kakakin sojojin ƙasar yace basu da niyyar cin zarafin wani, amma kuma ba za su lamunta da ci gaba da boren adawa da gwamnati da kuma ta'addanci ba. Dama dai tun a jiya shugaban askarawan sojan Masar ya nemi da a fito kan titi a gobe domin baiwa sojoji hallarcin murgushe duk mai adawa da su hukuma wanda ke neman tada ƙayar baya. Ƙasashen duniya dai na ci gaba da fargaban cin zarafin ɗan Adam, bisa wannan kiran da babban hafsan ya yi na a fito zanga-zanga, abinda ke nuna alamun hukuma na son yin amfani da karfi kan masu yi mata taurin kai.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu