Rikicin Mali ya raunana tarihin birnin Timbuktu | Zamantakewa | DW | 13.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Rikicin Mali ya raunana tarihin birnin Timbuktu

Birni mai daɗaɗɗen tarihi da ke tsakiyar Mali, ya fita hanun masu kaifin kishin addini, amma har yanzu al'ummar na zama cikin tsoro da talauci, sakamakon ɗurkushewar tattalin arziƙi

A hukumance, Timbuktu, birni mai daɗaɗɗen tarihi a arewacin Mali ya fita daga hannun 'yan tawaye, kuma a yanzu haka dakarun Mali na tsakiyar birnin a yayinda dakarun Faransa suke wajen birin, can a filin jiragen sama. To sai dai duk da haka, babu abubuwan da suka wajaba, waɗanda suka haɗa da tsabtataccen ruwan sha, wutar lantarki da abinci, kuma har wa yau al'ummar na zaune cikin tsoro da fargaba.

Wannan ɗaya daga cikin wuraren binciken dakarun Mali ke nan a tsakiyar Timbuktu, a kan titin kuma akwai motocin akori kura guda biyu a tsaye na 'yan tawayen da aka yi galaba kansu, amma kuma kamar dai yadda aka saba tun daa, duk wanda ya zo za'a marabce sa da harshen Faransanci da kuma Larabaci

Ali Baba wani wanda daa yake nunawa waɗanda suka zo yawon buɗe ido wurare a Timbuktu, ya ce ba hubbaren waliyai suka rusa da kuma takardu masu tarihi suka ƙone kaɗai ba, sun ɗauki tsawon shekara guda suna firgitar da mutane, sun haramta su yi abubuwa, sun kuma riƙa yanke musu gaɓoɓi suna kuma jifansu, duk wannan ya zama tarihi amma kuma wahalar da suka bari a baya na nan, daga farkon watan Fabrairu, lokacin da shugaban ƙasar Faransa Francois Hollande ya ɗauki nauyin 'yantar da birnin, tana cikin wani hali amma ya zuwa yanzu, Faransawa kaɗan ne ke kan titunan ƙasar.

"Timbuktu na cikin wani yanayi na ɗimuwa, kusan ba abunda zai sake kasancewa kamar yadda ya ke a farko. Da Kowa ya san kowa, kuma a shirye suke su taimake ka, suna kuma sha'awan karɓar baƙi, amma yanzu, kowa kansa ya sani, yadda zai ceci kansa, haɗari na da yawa, mutane da yawa sau daya suke cin abinci, idan ma sun samu ke nan"

A cikin kasuwa, mutane da yawa na tallan kayayyakinsu amma babu mai saye hakanan ma lemun zaƙin da Binta Maiga ke saidawa duk sun ruɓe a cikin zafi.

"Dole ne in ƙara farashin, saboda ni mana saye shi da tsada, ba 'ya 'yan itace, da kayan lambu kaɗai ba, har da suga da mai. kuɗin dukkansu ya riɓanya kuɗin da ake sayowa kafin yaƙin, hanyoyin samun ma yanzu babu saboda hnyoyin ma sun lalace kuma akwai hatsarin gaske saboda abubuwa masu fashewa da aka sanya a hanyoyin, kuma iyakokin mu da Aljeriya da Mauritaniya a rufe suke, mutane basu da aiki kuma basu da kudi"

Kasuwanci a ɓarayin da yafi yawan larabawa duk ya durƙushe duk wani mai farin fata ana zarginsa da haɗa kai da 'yan tawayen, ko kuma masu sayar da makamai ko masu sayar da miyagun ƙwayoyi ko kuma ma masu ƙunar baƙin wake. Dakarun Malin sun cafke wasu fararen fata da Abzinawa wadanda daga baya aka ga gawawwakinsu aka yi maza-maza kuma a rufe su cikin ƙasa a wajen gari. Ali Ould Mohammed Kabadi na ɗaya daga cikin irin waɗanda aka kama, ɗan sa Ibrahim mai shekaru 16 na haihuwa na cikin ruɗani kasancewar shi kaɗai yake kula da ƙannensa maza guda biyu

"Ina so in san gaskiyar, bana iya baci, bana iya cin abinci, kowa a Timbuktu ya san mahaifi na, ɗan asalin wannan birnin ne kuma ya yi imani da Mali, amma yanzu ya rasu, ni ina so in san takamaimai abunda ya faru.

Wannan yaƙi ya kawo ɓacin rai sosai a Timbuktu, wannan wuri mai ɗinbin tarihi da yawancin ƙabilu suka yi shekara da shekaru suna zama cikin lumana.

Mawallafiya: Alexander Göbel/Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Yahouza Sadissou Madobi