1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Sharhin jaridun Jamus kan Afirka

Usman Shehu Usman
October 1, 2021

Yawaitar juyin mulki a yankin yammacin Afirka da yunkurin dauko sojan hayar Rasha a kasar Mali sun mamaye jaridun Jamus a sharhunan da suka rubuta kan nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/419Es
Mali | Ankunft Choguel Kokalla Maïga in Bamako
Shugaba Assimi Goïta da Choguel Kokalla Maïga a fadar shugaban kasaHoto: Pressedienst des Premierministers

Za mu fara ne da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, wace ta yi labari kan kasar Mali. Jaridar ta ce duk da matsin lamba da jan kunne daga kasashen Turai, amma shugabannin soja na kasar Mali su n yi gaban kansu, sun  baiwa sojan haya daga kasar Rasha damar shiga su yi ayyukan wanzar da zaman lafiya. Wato rundanr Wagner mai zaman kasa, ko da shike ba ta cikin rundunar sojan Rasha a hukamance, amma kuma kowa ya san cewa rundunar ta samu goyon bayan gwamnatin Rasha. Shugaban sojojin da suka yi juyin mulki Assimi Goïta dan shekaru 38, da farin ya amince bisa matsin lamba ya mika mulki wa farar hula, amma watanni tara bayan haka ya kori Bah N'Daw da ke jagorantar gwamnatin, inda ya nada kansa ya ci gaba da jagorantar gwamnati.

Yawan juyin mulki a yammacin Afirka

Jaridar die tageszeitung ta ce zaben kuri’ia a wassu kasashen bayan kawo zaman klafiya, die tageszeitung ta yi misali da kasar ta Guinea, an kashe  mutane da yawa an kama wasu mutanen da dama bayan zanga-zangar kin jinin sauya kundin tsarin mulki, kuma hakan ya baiwa sojoji dama na kifara da gwamnati, jaridar ta ce sojojin kasar sun yi amfani da rashin zaman lafiya suka kifar da gwamnatin Alpha Conde, wanda yayi tarazce duk da kin haka da yan kasar suka yi. Wannan shi ne abinda yasa juyin mulkin ya samu farinjin yan kasar.

Kwatankwacin kyatar zaman lafiya ta Nobel

Marthe Wandou Preisträgerin 2021 des Right Livelihood Award
Marthe Wandou da ta samu lambar yaboHoto: Right Livelihood

Jaridar Neues Deutschland ta yi labarinta ne bisa kyatar kwatankwacin kyatar zaman lafiya ta Nobel da ka bawai Marthe Wandou yar kasar Kamaru. Wannan dai ita ce mace ta farko da ta samu irin wannan kyatar a kasar Kamaru, kai a duniya ma ita ce ta biyu bayan ‚yar kasar Sewden Greta Thunberg mai fafitikar kare mahalli da ta samu kyatar a shekara ta 2019. 'Yar shekaru 57 da haifuwa, Wandou ta kafa kungiyarta ne a shekara ta 1998 bisa yaki da banbancin jinsi tsakanin maza da mata, ayyukanta su ne kula da ilimin mata, da agaza wa wadanda aka ci zaf´rafinsu walau a yaki ko kuma wani tashin hankali. 

Cin zarafi karkashin hukumar lafiya ta duniya

Wani korofin da aka yi a Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango, na cin zarafin mata lokacin yaki nda annobar Ebola ya tabbata. Bayan korofin ne dai aka kafa kwamiti mai zaman kansa karkashin Aïchatou Mindaoudou tsohuwar ministar horkokin wajen Jamhuriyar Nijar, inda kwamiti ya gano cewa tabbas akwai jami’an WHO da ke da hannu wajen yin lalata da mata. 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani