Rikicin Libya har yanzu ba ta sauya zani ba | Siyasa | DW | 01.09.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rikicin Libya har yanzu ba ta sauya zani ba

Watanni takwas da karewar wa'adin da Majalisar Dinkin Duniya ta yanke na ficewar sojojin haya da dakarun ketare daga Libiya, har yanzu bata canja zani ba.

Kamar yadda ministan harkokin wajen Libiya Najla Al- Mangush ya fada a taron kasashe maqkwabtan Libiya da aka kammala a birnin Aljez na Aljeria, babu yadda za'a samu walwalar gudanar da sahihin zabe a kasar, muddin dakarun ketare ne da sojojin hayan ke iko da lamarin tsaron kasar.

Wasu kasashen dake makwabtaka da Libiya dai cikinsu har da Aljeriya na fargabar janye mayakan sa kai haka kwatsam kafin gudanar da zabe, kan iya bawa 'yan ina da mulki irinsu janar Haftar kwace ikon kasar da karfin tuwo. A yayin da wasu ke ganin cewa,Turkiya ba za ta janye mayakanta ba, muddin ba ganin an zabi sabuwar gwamnatin da za ta kare mata muradunta a kasar dama yankin ba.

Galibin masharhanta dai na danganta kasa fitar da sojojin daga kasar ta Libiya ga takaita fitar da kudurori na kasa da kasa ba tare da fayyace yadda za a aiwatar da wadannan kudurorin a aikace ba kamar yadda Abdulhadi Atwan editan jaridar Alsharqu ausat ke fadi: 

"Kamata yayi a ce kasashen duniya su yabawa dakarun Turkiya wadanda suka hana kisan kare dangi da mayakn haftar ke shirin yiwa mazauna Tripoli wanda yake son sake kafa mulkin kama karya fiye da na Gaddafi muni. Taraddadin da ake tayi kan rabe zare da abawa shi ke jawo tangarda a yunkurin fitar da mayan kan sa kai daga Libiya."

Shi ma Muhammad Abul Fadl na jaridar Al-Arab ga abun da yake cewa "Kowa ya San wadanda ke shigar da mayakan sa kai Libiya da kasashen Rasha da Siriya da Sudan da Chadi. An kuma san wadanda ke kokarin kwatar mulki da karfin tuwo. An kuma San wadanda suka lamunta da halascin taron Berlin da masu fatali da shi. Ko dai mu kira komai da sunansa don daukar matakin da ya wajaba, ko kuwa mu yi ta yin watangaririya da ma kasa warware wannan matsalar.

A daura da haka, wasu na ganin cewa rashin cimma matsaya kan dokar zabe da za ta fayyace yanayin 'yan takarar da masu iya zama sabin shuwagabannin Libiya, shine ummul haba'isin kasa kwance damarar sojojin haya koma korarsu daga kasar, yadda dokar hana masu shaidar zama 'yan kasashe biyu za ta hana janar Haftar takara, kasancewarsa yana da shaidar zama dan Amurka wanada a watan da ya gabata ya yi atisayin soji, yana mai shan alwashin yakar duk wata gwamnatin da aka yi kokarin kakabawa 'yan kasar daga ketare.
 

Sauti da bidiyo akan labarin