Rikicin karbe iko da kudancin Somaliya | Labarai | DW | 29.06.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin karbe iko da kudancin Somaliya

Rahotanni daga Kismayo a Somaliya na cewar mutane da dama galibi fararen hula sun rasu sakamakon fada tsakanin wasu kungiyoyi masu dauke da makamai.

Copyright für alle Bilder: Bettina Rühl (Zulieferer). Eins der Begleitfahrzeuge von Abdirahman Mohamed Farole, Präsident von Puntland, einer teilautonomen somalischen Republik

Konflikte in Somalia

Rikicin dai ya faru ne tsakanin 'yan bindigar da ke biyayya ga tsohon mai kaifin kishin addinin nan Ahmed Madobe wanda ya nada kansa a mastayin shugaban kudancin Jubaland da ke Somaliyan da kuma wadanda ke tare da Bare Hirale, tsohon ministan tsaron kasar wanda yanzu haka ya ke jagorantar wata babbar kungiya ta 'yan bindiga.

Mazauna wannan yakin da fadan ya wakana dai sun ce yanzu haka kura ta fara lafawa inda suka ce ya zuwa yanzu mutane kimanin goma sun rasu baya ga wasu da dama da suka jikkata.

Tuni dai hukumomi suka yi kira ga bangarorin biyu da su aje makamansu inda wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Somaliyan Nicholas Kay a wata sanarwa ya bayar a wannan Asabar din ya shawarci bangarorin biyu da su guji duk wani abu da zai kai ga tsoma kasar cikin wani hali.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal