Rikicin kabilanci ya barke a Kwango | Labarai | DW | 03.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin kabilanci ya barke a Kwango

An ba da rahoton cewar mutane akalla 49 suka rasa rayukansu a cikin rikicin kabilanci a lardin Ituri da ke a yanki arewa maso gabashin Jamhuriyar Demokaradiyar Kwango yayin da wasu dubbai suka yi kaura daga yanki.

Masu aiko da rahotannin sun ce fadan da aka gwabza tsakanin makiyya 'yan kabilar Lendu da manoma 'yan kabilar Hema ya rutsa da mata da kuma yara kanana. Fada tsakanin kabilun Lendu da Hema wanda ke zaman tsohuwar gaba a tsakaninsu tun daga shekara ta 1999 ya yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu sitin kawo yanzu.