Rikicin jihar Rivers ya ƙi ci ya ƙi cinyewa | Siyasa | DW | 26.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rikicin jihar Rivers ya ƙi ci ya ƙi cinyewa

Majalisar dattawan Najeriya na jiran jin rahoton kwamitin da ta tura jihar Rivers dan samun hujjojin da za su taimaka wajen warware matsalolin da suka turniƙe fagen siyasar ƙasar

A wani abun dake zaman karatu na nadama, shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonatahn ya ce yana shirin shiga makarantar ta natsu da nufin samo amsar lissafin da ya birkice cikin jihar Rivers dake zaman abun hayaniya ga kowa a kasar.

Sannu a hankali dai tasarin rikicin na daɗa bayyana a idanun masu ruwa da tsaki a cikin sa, sannu a hankali kuma nadama na neman zama salatin dake bakunan su, ga mahukuntan tarrayar Najeriya da suka ɗauki alƙawarin sauyi da nufin sake tabbatar da zaman lafiya cikin siyasar Rivers.

Shugaban ƙasar Goodluck Ebele Jonatahn da 'yan majalisar dattawan ƙasar suka ambato a matsayin kanwa uwar gamin rikicin dai, ya ce ya damu kwarai, kuma yana shirin nazarin rahoton rikicin, da nufin ɗaukar matakin kaishi ga ƙarshe cikin ɗan kankanen lokaci.

Jonathan ɗin dai ya shaida wa shugabannin lauyoyin ƙasar ta Najeriya cewar fa ɗagun haƙarƙari kan batu na zaɓukan shekara ta 2015 tun daga yanzu a Najeriyar dai abu ne dake tada hankali da kuma zai yi iyakacin ƙoƙarinsa domin maida shi tarihi.

Sassa daban-daban a ciki da wajen ƙasar ta Najeriya dai na kallon gazawa a ɓangaren 'yan siyasar da suka faɗa dajin ko mutuwa ko yin rai da nufin tabbatar da ikon su cikin harkokin siyasar ƙasar ta Najeriya, abun kuma da a cewar shugaban ƙungiyar lauyoyin kasar Okey Wali da ya jagoranci wata tawagar da ta gana da shugaba Jonathan ɗin ke zaman babbar matsalar da ka iya fuskantar tsarin da ƙasar ta kai ga samun shekaru 14 farko jere cikin sa .

"Mun bayyana damuwar mu da abun dake fitowa daga jihar Rivers, kuma mun roƙi shugaban ƙasa da yayi duk abun da yake iya yi cikin doka domin tabbatar da zaman lafiya ya sake dawowa cikin garin Fatwakwal. Sannan kuma doka da oda sun ɗore. Haka kuma a duk lokaci dole a bi doka mun bayyana wannan ƙarara ga shugaban ƙasar tarayyar Najeriya."

Martanin Lauyoyin da ke shiga tsakani

Damuwar lauyoyin dai na zaman ta baya baya cikin jerin martanin da yanzu haka rikicin jihar ke haifarwa a ciki da ma wajen ƙasarta.

Tuni dai dama ita ma majalisar dattawan Najeriyar da ta tura wani kwamitin zuwa garin na Fatakwal ya kuma dawo da rahoton dake tabbatar da zargin hannu na shugaba Jonathan a cikin rikicin ta bayyana karɓe ɗaukacin aiyyukan majalisar dokokin har nan da tsawon wasu wattani uku masu zuwa.

Nigeria / Goodluck Jonathan / Präsident

Goodluck Jonathan

Senator Abdul Mumini Hassan dai na zaman ɗaya daga cikin dattawan da suka je garin domin bin ba'asin abun da ya faru. Kuma a cewar sa sun hango hannu da ma ƙafar matar shugaban ƙasar cikin rikicin duk da kokari na nisan ta mazauna fadar gwamantin ta Aso rock da a bun dake faruwa a cikin birnin.

"lissafi na biyar yana gaban 22 ko kuma 16 tafi sha tara dai na zaman sabon lisafin da ya shiga cikin zuciyar masu mulkin tarrayar Najeriyar abun kuma da ake ta'allakawa da tashe tashen hankulan da suka tilasta wasu gwamnonin kasar biyar na jamiiyar PDP karade ko'ina domin neman hanyar sake saita lissafin kowa"

To sai dai kuma a cewar Garba Umar Kari dake zaman wani masani na siyasar Najeriya amincewar shugaban ƙasar na komawa makarantar lissafin na zaman gagarumin cigaba a ƙoƙarin sake tabbatar da saitin kowa cikin kasar.

Babban kalubalen dake gaban shugaban dai na zaman rawar dattaku dama tofin Allah tsine ga muƙarrabansa dake da ruwa da tsaki a cikin rikicin tare da fuskantar barazanar asarar goyon bayansu cikin burin sa na sake mulkin ƙasar a nan gaba.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Pinaɗo Abdu Waba

Sauti da bidiyo akan labarin