Rikicin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya | Labarai | DW | 04.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

Akallah mutane 12 aka kashe a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, ciki kuwa harda kananan yara da kuma wata mata mai dauke da juna biyu.

Kiristoci masu dauke da makamai sun kai hari a yankin yankin Peuhl, da ya kasance yankin Musulmi tsiraru, wanda ke kimanin kilomita 95 da arewacin babban birnin kasar Bangui, inda suka kashe mace guda dake dauke da juna biyu da kuma kananan yara 10, a dai dai lokacin da ake fargabar barkewar rikicin addini a kasar da ta sha fama da yaki.

Wadannan hare-haren dai na zuwane a dai dai lokacin da Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, ke shirin kada kuri'a dangane da kaddamar da gagarumar rundunar wanzar da zaman lafiya a kasar, da ke fama da rikici tun bayan da 'yan tawayen seleka suka kifar da gwamanati tare da tilasatswa hambararren shugaban kasar, Francois Bozize yin gudun hijira.

Mawallafi: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu