Rikicin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya | Labarai | DW | 05.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Wasu jami'an hukumar bada agaji na Majalisar Dinkin Duniya na barazanar fita daga yankin arewacin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, inda suka ce tabarbarewar tsaro na tilasta wa ma'aikatan agaji da dama kauracewa yankin.

Shugaban kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Faustin-Archange Touadera

Shugaban kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Faustin-Archange Touadera

Hukumomin bada agaji a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun ce koda yake babu rayukan jami'ansu da suka salwanta kawo yanzu, amma jerin hare-hare 33 a fadin kasar da 'yan bindiga suka kai kan kungiyoyi masu zaman kansu daban-daban na ci gaba da haddasa fargaba ga ma'aikatan hukumomi da ke aikin agaji a kasar.

Duk da albarkatun Lu'u-Lu'u da kasar ke da shi, al'ummarta na fama da talauci, inda hukumar bada agaji ta Majalisar Dinkin Duniyar ta kiyasta cewa mutane sama da miliyan biyu da ke wakiltar rabin al'umar kasar na bukatar agaji a halin yanzu. Tun a shekara ta 2012 Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar ta fada cikin tashin hankali da ke da nasaba da rikicin addini sakamakon yawaitar makamai a hannun kungiyoyi masu gwagwarmaya da makamai.