1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

October 10, 2013

Shugaba Michel Djotodia na Jamhuryair Afirka ta Tsakiya ya yi buris da duk wani tayin taimako daga ƙetare duk kuma da wadi na tsaka mai wuya da ƙasarsa ta faɗa ciki.

https://p.dw.com/p/19xdU
Hoto: picture alliance/landov

Rikicin tawaye da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ke fama da shi na ci gaba da ta'azzara duk kuma da kafa gwamnatin rikon ƙwarya da aka yi a wannan ƙasa. Hasali ma dai dubban 'yan ƙasar ne suka ƙaurace wa matsugunansu tare da fakewa a ƙasashe makwobta ciki har da Kamaru. Tuni ma dai suka tsinci kansu ciki wani mawuyacin hali a kan iyakar ƙasarsu da gabashin Kamaru, inda har yanzu 'ya'yansu ba su fara karatu ba. Dalili kuwa shi ne hukumomin wannan ƙasa sun bayyana cewa babu isassun gurabe a makaratun wannan yanki. Saboda haka ne ma shugabar reshen hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya a kamaru Ndeye Ndiougou ta yi tattaki i zuwa sansanin 'yan gudun hijiran Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya domin gane wa idanunta halin suke ciki.

"Sun yanke shawarar kaurace ma sansanin 'yan gudun hijira domin zuwa tare da zama a kauyen Borogo. kashi 80% na 'yan gudun hijiran matasa ne. Sannan kuma kashi 70% na bukatan zuwa makaranta. Sai dai babu makarantu a sansanin Nadunge."

Unruhen in der Zentralafrikanischen Republik
Han yanzu babu zaman lafiya a Jamhuriyar Afirka ta TsakaiyaHoto: P.Pabandji/AFP/GettyImages

Makasudin Ziyarar janar Gaye a Kamaru

'Yan gundun hijiran Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya dubu uku ne ke tsugune a Nadunge, yayin da a jimilce dubu 50 suka shigo ƙasar ta Kamaru tun bayan ɓarkewar rikicin baya-bayannan. Wannan dalili ne ma ya sa Majalisar Ɗinkin Duniya nuna fargaba game da tabarbarewar ayyukan jin kai a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Ko da shi ma Janar Boubacar Gaye manzon da sakataren MDD ya aiko Kamaru, sai da ya ce har yanzu akwai sauran rina a kabao a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

"Al'amura na ci-gaba da tabarbarewa yanzu haka a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ya taɓarɓare, saboda ƙasar ba ta da karfin tafiyar da rundunar sojojinta yadda ya kamata. Sai dai akwai yunƙurin dipolomasiya da ya kamata a yaba da ƙasashe makowbtanta suka yi domin cetota daga halin da ta ke ciki. Amma kuma ana ci gaba da samun tashe-tashen hankula saboda wasu dakaru ba sa samun albashin daga gwamnati. Maimakon shaka suna samun kuɗin shiga ne daga tursasa wa jama'a da suke yi."

Shugaba Djotodia na kunnen uwar shegu

Boubacar Gaye ya yi kira ga ƙasashen da ke makwabtaka da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da su kai mata ɗauki da ta ke buƙata musamman ma a fannin tsaro. Wannan ziyarar ta manzon sakataren MDD a Kamaru, ta zo ne bayan da shugaba Michel Djotodia ya bayyana yayi wani taron manaima labarai cewa gwamnatinsa na da karfin murkushe waɗanda ya danganta da kananan kwari.

Umsturz in der Zentralafrikanischen Republik Seleka Rebell
'Yan tawayen SELEKA na cin karensu babu babbaka a BanguiHoto: AFP/Getty Images

"Ba za mu zuwa ido mu jira wani taimako daga ƙasashen ƙetare. ba Za mu iya zaƙulo waɗannan 'yan fashi da kanmu. Mu dibar musu wa'adin watanni uku na miƙa masu da kansu cikin girma da arziki. Mun san idan suke. Mun yanke shawarar sa kafar wando guda da su har sai mun ga mun kare dokiyoyin al'uma da rayukansu."

Tun dai bayan da shi Michel Djotodia ya ɗare kan karagamar mulki sakamakon hambarar da gwamantin Francois Bozize, buƙatu na jin kai ke daga karuwa a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe

Edita: Abdourahmane Hassane