Rikicin Isra´ila da Falasɗinawa | Labarai | DW | 20.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Isra´ila da Falasɗinawa

Isra´ila ta sake kai farmaki ta sama a Zirin Gaza

default

Wakilan ɓangarori huɗu da suka halarci taron samar da zaman lafiyar Gabas Ta Tsakiya a birnin Mosko

Sojojin Isra´ila sun sake kai hari ta sama akan wani filin jirgin sama da ba a amfani da shi dake Zirin Gaza. Ma´aikatan ceto na Falasɗinawa sun ce aƙalla mutane 11 sun samu raunuka biyu daga ciki rauni mai tsanani sakamakon wannan hari. A jimilce rokoki huɗu ne aka harba kan filin jirgin saman dake kusa da birnin Rafah dake kudancin Zirin na Gaza. A ranar Alhamis da ta gabata wani manomi ya mutu a wani harin makami mai linzami da Falasdinawa suka kai a kudancin Isra´ila.

A wani labarin kuma ministan harkokin wajen Isra´la Avigdor Liebermann yayi watsi da sabuwar shawarar da ɓagarorin nan huɗu kan yankin Gabas Ta Tsakiya suka bayar na fara sabbin shawarwarin zaman lafiya da kuma batun sulhun na ƙasashen biyu. Ya ce ƙasarsa ba za ta yarda da wasu tsare tsare marasa ma´ana ko tilasta mata aiki da wani tsarin lokaci ba.

Ita kuwa a nata ɓangaren hukumar mulkin cin gashin kan Falasɗinu ta yi maraba da shawarar kamar yadda aka ji daga bakin babban mai shiga tsakani na Falasɗinu Saeb Erekat.

"Muhimmin batu shi ne Isra´ila ta mutumta yarjejeniyoyin da aka cimma. Amma abin da muka gani kawo yanzu shi ne Isra´ila na fatali da dukkan ƙa´idojin. Ana buƙatar wani ƙwaƙwaran tsarin sa ido don hana gwamnatin Isra´ila ci-gaba da gina sabbin unguwanni."

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Yahouza Madobi