1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Israela da Lebanon

Saleh Umar SalehJuly 14, 2006
https://p.dw.com/p/Btz9
Gadan da Israela ta rusa a Beirut
Gadan da Israela ta rusa a BeirutHoto: AP

Dakarun sojin Izraela sun sake afkawa filin saukan jiragen sama na Lebanon dake Beirut da titunan motoci da cibiyoyin samarda wutan lantarki da na sadarwa,da hare haren dake da nufin neman yan Hizbolla su saki sojojin su biyu da sukayi garkuwa dasu,baya ga wasu 8 da suka kashe .

Fararen hula guda 4 ne suka rasa rayukansu,ayayinda wasu guda 63 suka jikkata daga hare haren dakarun na Izraela a yau jumaa,wanda ya kawo ga adadin mutane 61 kenan ,kawo yanzu suka rasa rayukansu da fara wannan rikici,kwanaki biyu da suka gabata.

Daga cikinsu dai,an kashe uku ne a kudancin Beirut,kana na hudun ya gamu da ajalinsa ne ayayin wani harin makami mai linzami daya fada kan gidansa dake birnin Bent Jbail.

A hare haren da suka kai da asubancin yau a Beirut din dai,dakarun Izraelan sun afkawa headquatan rundunar sojin dake yankin yan shai a kudanci,dakuma kadoji dake kan hanyar zuwa filin saukan jiragen sama da cibiyar samarda wutan lantarki.

Izrelan ta fara kaddamar da wadannan hare hare akan Lebanon ne bayan cafke dakarun sojinta guda biyu da kashe wasu guda 8 da yan hizbollah sukayi ranar laraba da safe.

Akwai yan kasar Kuwaiti guda biyu da maaikacinsu na cikin gida daga yankin Asia guda,da suka gamu da ajalinsu a wannan rikici a Beirut.Bugu da kari an kashe biyu daga cikin mayakan na hizbollah ,ayayinda a bangaren Izraela kuma mutane biyu ne suka rasa rayukansu,kana wasu faraen hula 50 sun jikkata,alokacinda yan hizbollah suka kai harin rokoki a garuruwan izraelan biyu dake arewaci,da suka hadar da Haifa.

Mayakan Hizbollah din dai sun harba rokoki kirar Katyusha guda goma sha bakwai a arewacin izraela a yau,saidai babu wanda ya samu rauni.

Shi kuwa ministan harkokin cikin gida na Izraela Ronnie Bar-On,yabawa dakarun izraelan yayi adangane da nasarar da suke samu na kaiwa Lebanon hare hare,wanda k eke bayyanawa gwamnatin Lebanon day an hizbullah cewa,su kanwar lasa bane,idan anyiwa harkokin rayuwa da tsaron alummarsu barazana.

To sai dai a hannu guda kuma sugaba George W Bush na Amurka ya yi alkawarin tursasawa Izraela dakatar da wadannan hare hare akan Lebanon.Shugaban Amurkan yayi wannan bayani ne a hiran da sukayi ta wayan tangaraho da Prime minister Fuad Saniora,a dangane da yadda lamura ke dada rinchabewa a yankin.

Kazalika prime ministan Britania Tony Blair shima yayi tsokaci dangane da bukatar samo bakin zaren warware wannan rikici.

“Hanya daya da zamu iya warware wannan rikici shine,mu marawa shirin majalisar dunkin duniya baya na samar da zaman lafiya a wannan rikici,kuma cikin gaggawa.Ina so in jaddada cewa wannan yana da muhimmanci matuka cikin harkokin tsaro da zaman lafiya a duniya”.