1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Habasha na daukar hankali a Jamus

Usman Shehu Usman MAB
November 12, 2021

Samun kafar sasanta rikicin siyasar kasar Habasha cikin sauki da kason kudi da ya kamata a ba wa kasashen Afirka don yaki da sauyin yanayi a taron COP26 na daga ciin baututuwa da jaridun Jamus suka maida hankali a kai.

https://p.dw.com/p/42uyL
Äthiopien | Treffen Getachew Reda, Olusegun Obasanjo und Debretsion Gebremichael
Hoto: Privat

Za mu bude sharhunan da rikicin kasar Habasha, inda Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce kila a samu kafar sasanta rikicin siyasar kasar Habasha. Yayin da yaki ya ci gaba da bazuwa a kasar, masu ruwa da tsaki na kasa da kasa na duba hanyoyin sasanta tsakanin abokan gaba. Wakilin da kungiyar AU ta nada ya jagoranci sasantawar, tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, ya ce ya ga kofar sasanta rikicin. Sai dai ya ce  babu lokacin da za a bata wajen yafyyaa wa rikici ruwa daga bangaren gwamnatin kasar da mayakan yankin Tiray da kawayensu. Obasanjo ya mika rahotonsa wa Sakatare Janar na MDD, bayan ganawarsa da bangaren gwamnati da mayakan Tigray har ma da wadanda ke a yankin Oromo, kuma ya ce sun nuna alamun son a magance rikicin ta hanyar tattaunawa.

 Kudi ga kasashen Afirka a taron sauyin yanayi na COP26

Ita kuwa jaridar Die Zeit, ta duba taron kare muhalli a Glasgow, inda ta ce kasashe masu tasowa za su so dimbin kudi na tallafi kan sauyin yanayi daga kasashen da ke da karfin arzikin masana'antu.Dama an bukaci kasashen su rika biyan dalar Amirka biliyan 100 a shekara, amma ba sa ciki wannan ka'ida. Kasashen Afirka sun kara tsaurara ka'idojin biyan kudin, inda tun farko fara taron na bana, kasashen suka ce yanzu fa an wuce lokacin yin magana a fatar baka kawai. Dama dai a taron sauyin yananyi na duniya da ya gudana a shekara 2015, kasashe masu karfin arzikin masana'antu sun yi wa kasashe masu tasowa alkawarin dala biliyan 100, a matsayin kudin kariya daga illar sauyin yanayi, wanda za rika bayarwa ko wace shekara kama daga bara. Amma kasashen da suka yi alkawarin sun rabe da batun annobar corona, inda baran abin da ya samu bai fi dalal biliyan 80 ba.

UN-Klimakonferenz 2021 in Glasgow | Felix Tshisekedi, Präsident DR Kongo
Shugaba Tshisekedi na Kwango na daga cikin wadanda suka yi jawabi a taron Cop26Hoto: Pau Ellis/AFP/Getty Images

 Allurar rigakafin corona ba ta wadata a Afirka ba

Sai kuma batun rigakafin annobar corona wanda jaridar Süddeutsche Zeitung ta yi sharhinta a kai. inda ta ce gwara a samu dan kadan maimakon a ce babu ko dan kadan, musamman a yanayin tashin hankali da Afirka ke fuskanta na karancin allurar rigakafi, ga kuma al'ummar nahiyar wacce ke matukar shakkar magungunan kasashen Yamma.Jaridar wace ta leka wani asibiti a Nouakchott, babban birnin kasar Mauritaniya, ta yi misali da yadda ta ga wasu mutane sun dan gamsu. Jaridar ta ce ga wasu 'yan kasar ta Mauritaniya, ba sun cewar ba sune kadai ke cikin irin wannan tashin hankali na rashin samun allurar rigakafi ba.

Malawi Impfung gegen das Corona-Virus
Malawi da sauran kasashen Afirka na fama da karancin allurar coronaHoto: Joseph Mizere/dpa/XinHua/picture alliance

Kafofin sada zumunta na bunkasa a kasashen Afirka

Sharhin Neue Zürcher Zeitung, ya yi waiwaye kan batun sadarwar zamani, inda labarin da jaridar ta yi ya ce manhajar Whatsapp ta maye gurbin yanar gizo a Afirka. A kasashen da suka ci gaba da wadanda ke tasowa, a yanzu kasuwar sadarwar zamani ita ce a gaba wajen habaka. A cewar jaridar sun ziyarci birnin Nairobin kasar Kenya, inda kan wani titin sayar da tayoyin mota da sauransu, suka leka wani shago mai akalla ma'aikata takwas, da suka leka wani shagon buga takardu. Hatta ma'aikatan suna wani kasunci a gefe ta shafukan Whatsapp. Abin da ke kara tabbatar da yadda rawuya ta koma bisa sadarwar zamani. Inda 'yan kasuwa kan tallata kayakin da suke kerawa ta shafukan WhatsApp cikin sauki.

WhatsApp, Telegram, Messenger Dienste, App-Icons, Anzeige auf Display von Handy, Smartphone, Detail, formatfüllend
WhatsApp da sauran kafofin sada zumunta na habaka a AfirkaHoto: Valentin Wolf/imageBROKER/picture alliance