Mali: Rikicin Fulani da 'yan kabilar Dogon
June 26, 2018Yanzu haka dai hukumomin Mali na kokarin shawo kan matsalar, sai dai kuma suna fuskantar suka daga 'yan adawa a kan wannan batu. Tun lokacin da aka fara yin tashin hankalin gwamnatin Mali ta sanar da cewar ta jibge sojoji a garin na Koumaga, inda ake faman yin tashin hankalin tsakanin Fulani da 'yan kabilar Dogon. Yanzu haka jam'ian gwamnati biyu na kasar ta Mali sun isa yankin domin kwantar da hankula. Babbar matsalar dai shi ne cewar wasu kabilun Fulanin na zargin hukumomin da nuna goyon baya ga maharban Dozos 'yan kabilar Dogon. 'Yan adawa dai na Malin na zargin gwamnatin da saka siyasa a cikin wannan rikici. Shekaru uku ke nan da suka wuce yankin Tsakiyar na Mali yake fama da tashin hankali na fadan da ake yi tsakanin makiyaya da Fulani da 'yan kabilar Bambara da kuma Dogon wadanda galibinsu manoma ne.