Rikicin Eritrea da Habasha | Labarai | DW | 17.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Eritrea da Habasha

Eritrea ta sake jaddada matsayinta dangane da kin amincewa da babban jamiin mdd,domin zuwa ziyarar gani da ido akan iyakar eritre da Habasha.A wata wasikar gargadi da data aikewa sakatare general Ban ki Moon ,gwamnatin Asmara ta zargi mdd da nuna son kai tsakaninta da Habasha,adangane da nadin Azouz Ennifar a matsayin jagorar ayarin lura tsakanin kasashen biyu.Asmara tace ayayinda mdd tayi laakari da kin amincewa da Habasha tayi adangane da wanda aka nada,tayi watsi a hannu guda da bukatun Eritrea.Kasashen Habasha da Eritre dai na cigaba da zargin juna ,tun bayan rattaba hannu a yarjejeniyar kkanniyakas,a shekarata 2000,wadda ta kawo karshen zubar da jini na shekaru biyu a tsakanin alumomin wannan kasa dake makwabtaka.