1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Mutum sama da 300 sun ji rauni

Ramatu Garba Baba
May 10, 2021

Mutum sama da 300 ne suka ji rauni a wannan Litinin da aka shiga rana ta uku ana gwabza fada a tsakanin Falisdinawa da Yahudawa.

https://p.dw.com/p/3tCdS
TABLEAU | Israel Jerusalem | Spannungen & Gewalt
Hoto: Ahmad Gharabli/AFP/Getty Images

Mutum sama da dari uku aka tabbatar sun ji mugun rauni a rikicin Isra'ila da Falisdinu. Asibitoci sun cika makil da wadanda suka ji rauni daga tashin hankalin inda lamarin ba ya nuna alamun sassautawa. Rahotannin sun sheda yadda 'yan sandan Isra'ila ke harba gurneti kan Falisdinawan da ke jifa da duwatsu, a yayin da su kuma manyan kasashen duniya ke sukar matakin sojin Isra'ila na amfani da karfi kan jama'a.

Ana ganin tun shekarar 2017, ba a ga rikici mai munin na wannan lokacin ba, tashin hankalin dai, ya soma ne a yayin da Yahudawa ke gudanar da wani tattakinsu na nuna kishin kasa a birnin na Qudus, wuri mai tsarki da duk addinan kasar ke girmamawa. Ana sa ran a wani lokaci a wannan Litinin, Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai yi wata ganawa kan rikicin.