1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin bayan zabe ya barke a kasar Benin

Mouhamadou Awal Balarabe ATB
June 10, 2019

Mazauna garin Tchaourou da ke arewacin Benin sun yi kone-konen tayoyi tare da yin arangama da jami'an tsaro bayan kama mutane biyu bisa zargin haddasa rikicin zabe na 'yan majalisa.

https://p.dw.com/p/3K9AW
Benin,  Krawalle in Cotonou
Hoto: Getty Images/Y. Folly

Rikicin ya barke a garin Tchaourou da ke arewacin Benin bayan da 'yan sanda suka kama mutane biyu bisa zargin haddasa hatsaniya a lokacin zaben 'yan majalisa da ya gudana makonnin da suka gabata. Mutane da dama sun fito kan tituna, inda suka kafa shingaye a kan hanya tare da lalata motar jami'an tsaro, bisa abin da suka kira bita da kullin siyasa. Sai dai an baza 'yan sanda da sojoji don kwantar da kurar rikicin.

A ranar 28 ga watan Afrilu ne tashin hankali ya barke a garin Tchaourou da ke zama mahaifar tsohon shugaban kasa  Boni Yayi  saboda rashin bai wa jam'iyyun adawa damar shiga zaben 'yan majalisa. Yanzu haka ma 'yan sanda sun kewaye gidan tsohon shugaban da ke birnin Cotonou bisa zarginsa da tunzura jama'a ga yin bore.

 Tun dai bayan zaben na kasar Benin, an kama mutane da yawa bisa zargin tashin hankali da ya haddasa mutuwar mutane akalla hudu. Sai dai Kungiyoyi kare hakkin bil'Adama sun yi tir da son zuciya da  shugaban kasa Patrice Talon ke nunawa tun bayan darewarsa kan kujerar mulkin kasar.