Rikicin ƙabilanci a arewa maso tsakiyar Najeriya
November 22, 2012Rahotannin baya-bayan nan dai sunce koda da safiyar wannan Alhamis ma dai wani rikicin ya kuma sake ɓarkewa tsakanin 'yan ƙabilar ta Eggon da Kwaro, inda akayi ƙone-ƙonen gidaje tare da hassarar rayuka da dama, kuma ya zuwa yanzu akasarin mutanen da suka sami raunuka an kaisu asibitin kwararu na Dr. Ɗalhatu Arab dake cikin garin lafiya domin samun jiyya.
Hasali ma dai rikicin ya taso ne sakamakon zargin wani matashi da satar Babur daga Unguwar Yakubu dake cikin garin Agyragu inda kuma yaje ya sayar da Babur ɗin a Ungwar kwaro dake garin na Agyaragu, kuma bayan gano babur ɗin ne sai yamutsi ya tashi tsakanin ɓangarorin ƙabilun biyu.
Kasancewar matasa daga ƙabilun ne wannan lamari ya shafa, wani dana zanta dashi ta wayar tarho dake da zama a Unguwar Yakubu cikin garin Agyragu yace dani an soma rikicin ne a gaban sa.
Nayi ƙoƙarin samun alƙaluma don sanin adadin mutane da suka mutu ta hanyar jami'an 'yansanda, to amma hakan yaci tura domin acewar su akwai waɗanda rikicin kan ritsa dasu a wajen gari wanda kuma basu da cikakken rahoto kai, to sai dai wani dattijo a ƙauyen daya nemi in sakaya sunan sa, yace dani yana shirin yaje garin Lafiya ne domin gujewa tashin hankalin kuma ya tabbatar min da mutuwar mutane takwas agarin na Agyaragu.
Rahotanni sunce ƙone-ƙonen da akayi a wannan Larabar, ya ritsa da gidajen wasu manya-manyan jami'an gwamnatin jihar Nassarawa. Na tautaunawa da kakakin gwamnatin jihar kan al'amura na mussaman Abdulhamid Kwarara wanda yace dani da safiyar yau suka je garin na Agyaragu tare da mataimakin gwamnan jihar, kuma yayi min karin bayani ta wayar tarho daga can kauyen na Agyaragu.
Yanzu haka dai an tura wasu ƙarin jami'an tsaro dake sintiri tsakanin Lafiya zuwa garin na Agyaragu mai nisan kilomita 20, daga birnin Lafiya, don tabbatar da ganin rikicin ya lafa.
Mawallafi : Abdullahi Maidawa
Edita : Saleh Umar Saleh