1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Rikici ya kunno kai bayan bacewar kaya a hukumar zaben Ghana

March 20, 2024

Jagorancin bangaren adawa a majalisar dokokin kasar Ghana, ya bukaci a gudanar binciken gaggawa a kan yadda na'urorin tantance masu zabe suka yi batan dabo daga hukumar zaben kasar.

https://p.dw.com/p/4dwla
'Yan kasar Ghana a sahun kada kuri'a
'Yan kasar Ghana a sahun kada kuri'aHoto: Xu Zheng/Xinhua News Agency/picture alliance

Na'urorin tantancewar ta biometric guda bakwai ne suka bata daga hannun hukumar zabe a kasar ta Ghana, al'amarin da 'yan adawar ke cewa ba lallai ba ne a tabbatar da sahihancin zaben shugaban kasa na bana idan ba a warware wannan matsala ba.

Hakan ya bayyana ne a cikin bayanan shugabar hukumar zaben a majalisar dokoki. Ana amfani da na'urorin ne wajen tantance sahihance masu zabe wadanda aka dauki bayanansu a lokacin yin rajista, kuma da hakan ne ake iya tantance duk mai kada kuri'a a ranar babban zabe.

TAkardun kada kuri'a a zaben Ghana
Hoto: AP

A kan jadadda batan na'urorin har guda bakwai ne jagoran bangaren adawar gwamnati a majalisar dokokin kasar Cassiel Ato Forson, yake cewa da walakin.

''Ina rokon hukumar binciken manyan laifuka da hukumar ‘yan sanda ta kasa, su fidda sanarwa a take dauke da cikakkun bayanai a kan inda ake kai a bincikensu kawo I yanzu''

Tun bayan kama aikin Malama Jean Mensah bayan ta gaji Charlotte Osei a matsayin shugabar hukumar zaben Ghana ne dai, ake ta samun kananan maganganu a game da tafiyar da ayyukan hukumar zaben kasar.