1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yajin aiki ya hana sufurin jiragen Ryanair

Zulaiha Abubakar
September 26, 2018

Kamfanin ya sanar da soke tashin jiragen da yawan su ya kai 190 a ranar Juma'ar nan mai zuwa sakamakon rashin cimma daidaito tsakanin shugabannin kamfanin da kungiyar ma'aikantan jirgin saman da ke yajin aiki.

https://p.dw.com/p/35VOp
Deutschland | Ryanair startet bald auch von Frankfurt am Main
Hoto: Reuters/K. Pfaffenbach

Tun da fari shugaban sashen kasuwancin kamfanin Kenny Jacobs ya bayyana cewar kamfanin na neman afuwar abokan huldarsa, wadanda tuni aka aike musu da sanarwar dakatar da tafiye-tafiyen jiragen kamfanin.

Daga nan sai ya roki masu fada a ji na kungiyar ma'aikatan da su ba shugabannin kamfanin goyon baya don warware danbarwar data kunno kai.

A kalla fasinjoji dubu 30 ne wannan mataki da kamfanin na Ryanair ya dauka zai shafa.