Gini: Rikici ya barke bayan baiyana sakamakon babban zabe
October 23, 2020'Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai saka kwalla a tarwatsa masu zanga-zangar adawa da sakamakon babban zaben da ya bai wa Shugaba mai ci Alpha Conde nasara. Rahotanni na cewa, an yi arangama a tsakanin jami'an tsaro da magoya bayan madugun adawa Cellou Diallo a unguwar Sonfonia da ke Konakry, babban birnin kasar.
Kididdigar da hukumar zaben kasar ta fita ya nunar da cewa, Shugaba Conde ya lashe zaben da wagegen tazara gabanin babban abokin hamayyarsa Cellou Dalein Diallo a zaben da aka gudanar a karshen makon da ya gabata. Ana dai zargi mahukuntan Ginin da bayar da umarnin datse kafar intanet bayan barkewar rikicin na wannan Juma'ar, wanda kuma ba sabon abu bane da gwamnatin ta saba yi a duk lokacin da aka sami barkewar rikici a kasar..