1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici Tigray na jan hankali jaridun Jamus

Suleiman Babayo MAB
October 21, 2022

Rikicin yankin Tigray na kasar Habasha da barkewar cutar Ebola a kasar Yuganda da batun cin hanci da rashawa a kasar Kwango na daga cikin batutuwa da suka dauki hankalin jaridun Jamus a wannan mako.

https://p.dw.com/p/4IWTG
Rikicin yankin Tigray na Habasha ya yi kamariHoto: UGC/AP/picture alliance

Jaridar Die Welt ta yi sharhi kan rikicin yankin Tigray na kasar Habasha inda ta ce ya zama babbar matsalar jin kai da siyasa a Afirka. Jaridar ta ce gwamnatin kama karya ta Iritiriya ta kira sojojin wucin gadi yayin da take ci gaba da taimakon kasar Habasha a wannan takaddama, kuma mutane na tserewa kamar abin da aka gani lokacin da gwamnatin Rasha karkashin Shugaba Vladimir Putin ta kira sojojin wucin gadi domin su taya kasar fadan da take yi da Ukraine. Tun karshen shekara ta 2020 ne fada ya barke tsakanin dakarun yankin Tigray da sojojin gwamnatin Habasha, inda dubban rayuka suka salwanta.

Lage in Burkina Faso I 2. Oktober 2022
Ana daga tutar Rasha a gangami a Burkina FasoHoto: Vincent Bado/REUTERS

Rasha na da angizo a Burkina faso?

Jaridar ta die Tageszeitung ta mayar da hankali kan kasar Burkina Faso inda ta ce shin akwai wata rawa da kasar Rasha ta taka a sabon juyin mulkin da sojoji suka yi? Ya dace a janye sojojin Jamus na rundunar Bundeswehr daga wannan yanki na Afirka? Ta kara da cewa wannan shi ne juyin mulki na biyu a kasa da shekara guda a kasar, kuma a lokacin zanga-zangar goyon bayan juyin mulkin, wasu mutane sun fito dauke da tutocin kasar Rasha.

An kifar da gwamnatin Lt. Kanar Paul-Henri Damiba inda Kyaftin Ibrahim Traoré ya zama sabon shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar ta Burkina Faso da ke yankin yammacin Afirka, bayan ya zargi tsohuwar gwamnati da gaza yaki da ta'addanci.

Kongo Beni Ebola-Opfer
Ana daukar mataki wajen binne wanda Ebola ta kasheHoto: Jerome Delay/AP/picture alliance

Ta ya ya za a shawo kan Ebola a Yuganda?

Jaridar die Tageszeitung ta kuma tabo barkewar cutar Ebola a kasar Yuganda. Jaridar ta ce gwamnatin kasar ta tabbatar da yin rejistar mutane 60 da suka kamu da cutar a kasa baki daya, yayin da a birnin Kampala fadar gwamnatin kasar kuwa aka samu mutane uku da aka gwada suna dauke da cutar.

Shugbaba Yoweri Museveni na kasar ta Yuganda ya bayyana matakan yaki da barkewar cutar ta Ebola, da suka hada da takaita zirga-zigar mutane a yankunan da aka samu barkewar cutar, tare da hana fita da dare a cikin yankunan da abin ya shafa. Mutane 24 suka mutu kana wasu 24 sun warke daga cutar ta Ebola da ta barke a Yuganda.

Picture gallery - the world’s most important forests
Hoto: M.Harvey/WILDLIFE/picture alliance

Sayar da dajin Kwango don gina makarantu

A nata bangaren, jaridar Neue Zürcher Zeitung ta yi sharhi mai taken Jamhiuiyar Dimukaradiyyar Kwango ta yi gwanjon dazukan kasar ga kamfanonin hakar man fetur. Amma kungiyoyin kare muhalli sun bayyana irin sakamakon da hakan zai haifar, yayin da gwamnatin kasar ta ce tana bukatar kudin gina makarantu da hanyoyi da asibitoci.

Jaridar ta kara da cewa gwamnatin Kwango na amfani da tsaffin hotunan dazukan wajen nuna cewa kamar yanzu aka dauka, lamarin da ke zama wani wasan kwaikwayo. Masu adawa da matakin gwamnatin kasar ta Jamhiriyar Dimukaradiyyar Kwango suna zargin cewa kudin da ake zaton za a samu za su kare kamar abin da aka gani a baya sakamakon cin hanci, inda kasar take sahun gaba na kasashe 'yan rabbana da wadatamu, duk da irin ma'adanai da take fitarwa zuwa kasashen ketare.