Rikici na ci gaba tsakanin Izira′ila da Palesdinawa | Labarai | DW | 10.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikici na ci gaba tsakanin Izira'ila da Palesdinawa

Babban jami'n Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya nemi kawo karshen rikicin Izira'ila da Palesdinawa

Sakatare Janar na MDD Ban Ki-moon ya shaida wa taron gaggawa na Kwamitin Sulhu cewa, ana neman hanyoyin sasantawa na gaggawa, domin kare barkewar yaki gadan-gadan tsakanin Izira'ila da Palesdinawa, wanda zai iya yaduwa sauran sassan Gabas ta Tsakiya. Kawo yanzu kimanin mutane 80 sun hallaka, yayin da Izra'ila ci gaba da kai hare-hare ta sama, bisa martani na rokokin da tsagerun kungiyar Hamas ke cillawa.

Izira'ila ta ce dakatar da cilla rokoki daga kungiyar Hamas ne kawai zai janyo ta dakatar da kai hare-hare. Kimanin rokoki 550 aka cilla cikin Iza'ila, yayin da ta kai hare-hare fiye da 500 ta sama, abin ya hallaka fiye da mutane 80, mafi yawa fararen hula.

Akwai wasu mutanen kusan 340 da suka samu raunika, yayin da aka lalata gidaje fiye da 150, sannan wasu mutanen kimanin 1000 suka tsere daga gidajensu.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Pinado Abdu Waba