Rikici a kan iyakar Mali da Nijar | Siyasa | DW | 27.02.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rikici a kan iyakar Mali da Nijar

Kasashen Nijar da Mali sun bayyana daukar sababbin matakan shawo kan matsalar tsaron da kasashensu ke fuskanta a kan iyakokinsu musamman a watannin baya-bayan nan.

Matsalar rikicin kabilanci tsakanin Fulani makiyaya da akasarinsu 'yan jamhuriyar Nijar ne da kuma Abzinawan kasar Mali dai, a 'yan kwanakin nan sun haddasa asarar rayuka masu dinbin yawa, kamar yadda Ministocin tsaron kasashen biyu su ka bayyana yayin wani taro da su ka gudanar a Jamhuriyar Nijar da nufin karfafa matakan tsaro na hadin gwiwa dake tsakaninsu a wani mataki na shawo kan matsalar da ke yin barazana ga zaman lafiyar alum'momin kasashen biyu dake makwabtaka da juna.

Cimma matsaya a taron

Mali Bamako Soldaten

Jami'an tsaron kasar Mali na sintiri.

Wannan taro wanda ya samu halartar ministocin tsaro da hafsoshin sojojin kasashen sauran masu ruwa da tsaki a harkokin tsaron kasashen biyu, ya duba hanyoyin karfafa matakan tsaron hadin gwiwar da kasashen biyu ke da shi a baya da zum'mar rage karuwar tabarbarewar harkokin tsaron da ake fuskanta tsakanin kasashen tsahon shekaru da dama. A karshen taron sun fitar da wasu shawarwari kamar yadda Ministan tsaron kasar Mali Malam Sumailu Bubey Maiga ya yi karin bayani.


Ya ce "Shugabannin sojojin kasashenmu da ke aiki a kan iyakokinmu za su rinka tuntubar juna lokaci zuwa lokaci domin daukar matakan tsaron bai daya, kamar irin na yin amfani da rundunar sojoji masu sintiri a kan iyaka ta hanyar yin amfani da rakuma wacce ta baiwa sojojin kasar Mali damar kutsawa cikin wasu yankunan kan iyakar da ba su leka ba tun a shekara ta 2011. Haka zalika mun tsaida cewa za mu hada karfinmu a guri daya domin taimakawa talakawa mazauna yankinta hanyar inganta rayuwarsu da nufin kwato su daga hannun kungiyoyi masu mugun nufi na cikin gida da akasarinsu na da alaka da kungiyoyin ta'adda wadanda sune ke haddasa wanann rikici a tsakanin alummomin da ke zaune lafiya kuma ina da kwarin gwiwar cewa matakan da mu ka dauka za su bamu damar kalubalantar matsalolin".

Shekaru da dama dai kenan da wanann yanki na arewacin jihar Tillaberi dake Jamhuriyar Nijar wanda ke kan iyaka da kasar Malin ke fama da rikicin kabilanci tsakanin Fulani makiyaya da kuma wasu kabilun kasar ta Mali musamman ma Abzinawa wanda kuma ke da nasaba da sace-sacen dabbobi.

Nomadenleben im Niger

Makiyayan Jamhuriyar Nijar na kiwo.

Ra'ayin kungiyar Fulani makiyaya

Kungiyar Fulani makiyayan Jamhuriyar Nijar na yankunan da ke makwabtaka da kasar Malin dai ta bayyana ra'ayinta a kan wannan taro da ya biyo bayan wasu fadace-fadacen da su ka lakume rayukan mutane kimanin 30. Da ta ke tsokaci kan wanann mataki na karfafa matakin tsaro na hadin gwiwar da kasashen biyu su ka dauka, kungiyar Filani makiyaya yankin jihar ta Tillaberi wadanda su ne lamarin ya fi shafa ta bakin shugabanta Malam Diallo Abubacar ta bayyana gamsuwarta da shirin, sai dai ta ce yana bukatar gyara. Abun jira a gani dai shine tasirin da wanann mataki da kasashen Nijar da Malin su ka sake dauka zai yi wajan magance matsalar
tsaron da ke addabar alum'momin kan iyakar kasashen biyu.

Mawallafi: Gazali Abdu Tasawa
Edita: Usman Shehu Usman/ LMJ

Sauti da bidiyo akan labarin