Rikici a jam′iyyar adawa ta Zimbabwe | Labarai | DW | 27.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikici a jam'iyyar adawa ta Zimbabwe

Jam'iyyar adawa ta Zimbabawe, MDC, ta dakatar da shugabanta abin da ya kawo rarrabuwar kai

Wani bangaren na jam'iyyar MDC mai adawa a kasar Zimbabwe ya dakatar da shugaban jam'iyyar Morgan Tsvangirai, saboda yadda yake neman zama dan kama karya, sannan ya kasa kawar da Shugaba Robert Mugabe daga madafun ikon kasar.

Sakatare janar na jam'iyyar Tendai Biti ya jagoranci bangaren da ya kawar da Tsvangirai, inda suka ce yana kauce wa kiranye-kiranyen neman sauyi, bayan tsayawa zaben shugaban kasa karo uku ba tare da nasara ba.

Tsvangirai dan shekaru 62 da haihuwa ke shugaban jam'iyyar tun kafuwarta a shekarar 1999, kuma wannan baraka da ta kunno kai ka iya rauni wa jam'iyyar ta MDC, yayin zabuka shekara ta 2018.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman