Sama da mutane 50 sun halaka
January 28, 2020Talla
Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya dai na ci gaba da fama da rigingimun kabilanci da na addini, a tsakanin masu gwagwarmaya da makamai, duk da kasancewar rundunar samar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a kasar.
Rahotanni na cewar sama da kashi biyu na yankunan kasar na karkashin ikon masu gwagwarmaya ne, rikicin da ya yi wa kasar katutu, ba ya rasa nasaba da kokarin mallakar albarkatun kasa da Allah ya huwacewa kasar.