1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Amazon na fuskantar turjiya daga kabilun Afirka ta Kudu

April 26, 2022

Attajirin da ya fi kudi a duniya kuma mai kamfanin Amazon, Jeff Bezos, na son gina hedikwatar kamfanin a Afirka a fili mallakin kabilu. Sai dai suna fargabar matakin zai raba su da filayen da suke wa kallo masu tsarki.

https://p.dw.com/p/4AS89
Südafrika, Kapstadt | Proteste gegen Bau vom Amazon Headquarter
Hoto: Rodger Bosch/AFP/Getty Images


Yan kabilar Khoi da 'San' na da'awar cewa ana gine-gine akan kasar da suka gada tun kaka da kakanni da ya ratsa tsakiyar gundumomi masu muhimmanci na Cape Town a Afirka ta Kudu. To amma babban kamfanin sayar da kaya ta yanar gizo na Amazon ya kuduri aniyar gina hedikwatarsa a mahadar kogunan Black River da Liesbeek River, da mutanen yankin ke dauka da daraja. 

Afrika | Indigene Völker: Endorois Volk, Kenia
Hoto: Tony Karumba/AFP/Getty Images

 A yanzu dai wata babbar kotu a Cape Town ta dakatar da aikin har sai an shigar da mutanen karkarar 'yan asali da abin ya shafa cikin lamarin. Kabilun dai na bukatar a  dakatar da aikin ne dungurungum wanda Amazon ya  tsara kashe zunzurutun kudi Euro miliyan 260.

Braley van Sitters wani dan gwagwarmaya na kabilar Khoi ya  ce "ba mu yarda ba mu amince ba da wannan aiki.'' Yana ganin ci gaba da kokarin gina ofis din Amazon a wurin bayan jama'ar yankin sun nuna illar hakan ga al'adunsu, rashin martabawa ne ga al'ummomin Afirka ta Kudu.


A can baya dai wannan wuri an yi amfani da shi a matsayin wurin wasan kwallon Golf na kungiyar River Club. A taswirar da aka tsara a yanzu za a gina gidajen kwana da kantuna da kuma ofisoshi sannan da hedikwatar kamfanin na Amazon a filin.

Südafrika, Kapstadt | Proteste gegen Bau vom Amazon Headquarter
Hoto: AFP via Getty Images


Mutane 1,000 ake sa ran za su samu aikin yi idan har aka samu hedikwatar ta Amazon a yankin. Wannan mataki ya zo daidai da kudurin  Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa na kokarin jawo masu zuba jari a cikin kasar domin samar da ayyukan yi.

Kamfanin da ke aikin a cikin wata sanarwa ya ce galibin yan al'ummar 'Khoi' da 'San' suna goyon bayan ayyukan da ake yi. Domin karrama al'ummomin, Amazon ya ce sun tsara gina katafariyar cibiyar yada labarai da gandun raya al'adu da kuma dakin wasanni da taruka.

"Tsirarun mutanen da ke adawa da aikin na yada karya game da ayyukan da ake yi da tasirinsa ga rayuwar al'umma da kuma zamantakewar tsirrai da sauran hallitu.'' in ji sanarwar da kamfanin na Amazon ya fitar.

Idan har kotu ta kammala ta janye dakatarwar da ta yi a kan ginin, ana sa ran kammala kashin farko na ginin cikin shekaru biyu masu zuwa. Sai dai a yanzu masu fafutuka sun ce za su ci gaba da gwagwarmaya domin kare kasarsu da kuma al'adunsu.