Riga kafin rikicin tattalin arziki a Turai | Labarai | DW | 19.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Riga kafin rikicin tattalin arziki a Turai

Ministocin kuɗi na ƙungiyar Tarayyar Turai sun cimma yarjejeniyar kafa wata cibiyar da za a ɗorawa alhakin duba halin da bankunan nahiyar suke ciki.

Ministocin sun cimma wannan yarjejeniyar ne sa'oi ƙalilan gabanin fara babban taron ƙungiyar da suka saba gudanarwa a birnin Brussels na ƙasar Beljiam, da nufin kare sake afkuwar rikicin tattalin arzikin da nahiyar ta faɗa a baya, kuma za a tallafa wa bankunan da kuɗaɗe ba tare da an ƙara kudin haraji da ake karɓa daga al'ummar ƙasashen ba, tare da rufe bankunan da suka gaza.

Kwamishinan da ke kula da harkokin hada-hadar kuɗi na ƙungiyar ta EU Michel Barnier ne ya bayyana hakan a wani rubutu da yayi a shafinsa na Twitter, inda ya ce yarjejeniyar na zaman mai ɗinbin tarihi tun bayan da aka kafa ƙungiyar.Za a gabatar da yarjejeniyar gaban shugabannin ƙasashen nahiyar da zasu gudanar da taronsu a nan da 'yan sa'oi ƙalilan, domin su amince da ita. Daga cikin shugabannin da ke halartar taron har da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, da ta fara wasu sababbin shekaru huɗu na mulkinta a karo na uku.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita:Abdourahamane Hassane