Republican na gaba a zaben Amirka | Labarai | DW | 05.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Republican na gaba a zaben Amirka

Jam'iyyar adawar ta Republican a Amirka ta samu rinjaye a majalisar dattawan Amurka, karon farko cikin shekaru takwas.

Wannan nasara ta babbar jam'iyyar adawa ta Republican a Amirka da ta samu kujeru 52, na zama manuniya ga irin koma baya da jam'iyyar shugaba Obama ke samu.

Joni Ernst daga lowa ta lallasa Bruce Braley na bangaren jamiyyar Democrats, abin da ya sanya jam'iyyar ta Republican ta samu kujeru bakwai daga yankin, abin da kuma ya sanya ta zama gaban jam'iyyar masu mulkin na Amirka.

Jam'iyyar ta Republican yanzu za ta jagoranci kujeru 52 na majalisar da za ta fara aiki a watan Janairu.

Mambobin na jam'iyyar Republican har ila yau sun kawar da wasu sanatoci uku na jam'iyyar Demokrats masu ci, sannan kuma suka sake lashe wasu kujerun hudu da a baya 'yan jam'iyyar ta Democtrats ke rike da su.

A cewar Senata Mitch McConnell da ke bisa layin zama shugaban masu rinjaye a majalisar, ya ce masu kada kuri'a sun kadu da ganin samun sabon shugabanci.