RENAMO za ta sake ɗaukar makamai | Labarai | DW | 05.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

RENAMO za ta sake ɗaukar makamai

Ƙungiyar 'yan tawaye ta RENAMO ta Mozambik ta yi barazanar sake ɗaukar makamai domin yin yaƙi da gwamnatin jam'iyyar FRELIMO.

Wani kakakin ƙungiyar Antonio Muchanga, ya ce sun kawo ƙarshen yarjejeniyar dakatar da buɗe wutan da aka cimma tsakaninsu da gwamnatin a duk faɗin ƙasar. RENAMO tsohuwar ƙungiyar 'yan yaƙin sari ka noƙe, wadda a shekarar 1992 ta rikiɗe zuwa babbar jam'iyyar adawa bayan shekaru 16 na yaƙin basasa, na zargin gwamnatin FRELIMO da rashin raba iko da ita.

Tun watannin da dama da suka wucce da shirin tattaunwa tsakanin gwamnatin da 'yan tawayen, masu neman wani kaso na muƙamai a cikin harkokIn soji da 'yan sanda ta cije a birnin Maputo.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Suleiman Babayo