Real Madrid ta zama zakara tsakanin kungiyoyin nahiyoyi | Zamantakewa | DW | 20.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Real Madrid ta zama zakara tsakanin kungiyoyin nahiyoyi

Wasan kwallon hannu na duniya da aka kammala inda Faransa ta samu galaba a gasar na mata gami da wasu fannoni na wasanni.

 

Sakamakon wasannin Bundesliga na Jamus, FC Kolon ta samu nasara kan Wolfsburg da ci 1 mai ban haushi. Augsburg da Frieburg sun tashi 3 da 3, sannan Hannover da Leverkussen sun tashi 4 da 4, kana Borussia Dortmund ta doke Hoffenheim 2 da 1.

Har zuwa yanzu kungiyar Bayern Munich ke jagorancin gasar na Bundesliga da maki 41, yayin da Schalke ke mara mata baya da maki 30, inda Borussia Dortmund take matsayi na uku da maki 28. Kungiyar Leverkusen tana matsayi na hudu, sannan Leipzig duk suna da maki 28 inda banbancin kwallaye ke tsakanin kungiyoyin.

A wasannan Premier Lig na Ingila da aka kara a karshen mako, kungiyar Manchester United ta bi West Brom har gida ta doke ta da ci 2 da 1.  Arsenal ta samu nasara kan Newcastle da ci 1 mai ban haushi. Manchester City ta yi kaca-kaca da kungiyar Tottenham da 4 da 1.

Har yanzu Manchester City ke jagorancin teburin na Premier da maki 52, yayin da Manchester United ke matsayi na biyu da maki 41, ita kuma Chelsea tana matsayi na uku da maki 38, sai Liverpool mai matsayi na hudu da maki 34, sannan Arsenal take mataki na biyar da maki 33.

A wasannin lig na La Liga na Spain da ke gudana Barcelona ta ragargaza Deportivo da ci 4 da 0. Ita kuwa Villarreal ta bi Celta har gida ta doke da 1 da nema, yayin da Las Palmas ta tashi 2 da 2 da Espanyol.

Inda muka duba wasannin kungiyoyin kasashen kungiyar Real Madrid ta sake zama zakara tsakanin kungiyoyin kwallon kafa na nahiyoyin duniya bayan lashe gasar da ya gudana a birnin Abu Dhabi na Hadaddiyar Daular Larabawa, ita dai Real Madrid daga Spain ta doke Al Jazira daga Brazil da ci 2 da 1. Real Madrid ta lashe wannan kofin kofuna, tare da zama zakara a wasu wasanni da dama cikin wannan shekara ta 2017.

A karshen mako ne aka kammala gasar guje guje da tsalle tsalle dama wasu wasannin na Ma'aikatun Gwamnatin Tarayya da sauran Hukumomi dake karkashin Gwamnatin har dari da talatin wadanda suka halarta. An dai share kwanaki goma a garin Bauchi inda aka gudanar da gasar wadda akeyi duk shekaara domin kara dankon zumuncin ma'akatan.

A karshe wasan Faransa mata na kwallon hannu sun lashe gasar duniya da aka kammala a birnin Hanburg na Jamus. 'Yan wasan na Faransa sun samu galaba kan 'yan wasan Norway mata da ci 23 da 21. Faransa ta kafa tahiri wajen lashe gasar na kwallon hannu na duniya na maza, kuma babu wata kasa da ta lashe wasan kwallon hannu na duniya na maza da mata lokaci guda, tun shekarar 1982, kimanin shekaru 35 lokaci da tsohuwar Tarayyar Soviet ta samu irin wannan nasara.