1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar ba ta muradin kashe kudi mai yawa

Gazali Abdou Tasawa
July 25, 2018

Kungiyar ta Chelsea dai ta tsaida farashin dan wasan mai shekaru 27 a kudi Euro miliyan 225

https://p.dw.com/p/324QK
Russland WM 2018 Belgien gegen Tunesien
Hoto: Reuters/C. Recine

Kungiyar Real Madrid na zawarcin dan wasan Chelsea Eden Hazard amma kuma ta nuna cewa ba ta da niyyar zuba kudaden da suka wuce kima wadanda kasuwar cinikin 'yan wasa ke ciki a baya-bayan nan.

Real Madrid dai na son sayen dan wasan a farashin miliyan 120 na Euro da kuma yi masa albashin euro miliyan 15 a shekara. Albashin da zai kasa wanda kungiyarsa ta Chelsea ta yi tayin ba shi idan ya tsawaita kwantaraginsa.

To sai dai dan wasan ya bayyana kurwarsa ta neman buga wa Real Madrid wasa kuma Chelsea ba ta buga wasannin zakarun Turai a kakar wasannin ta gaba, lamarin da ka iya yin tasiri wajen tilasta wa kungiyar ta Chelsea sayar da wasan.