RDPC ita ce jam'iyyar da ke mulki a Kamaru. Shugaban Kamaru Paul Biya ne ya kafa ta a 1984 don ta maye gurbin jam'iyyar UNC da wanda ya gabace shi ya kafa.
Tana da cikakken rinjaye a majalisar dokoki da ta dattawa. Shugaba daya wannan jam'iyya ta samu tun bayan kafata, wato Paul Biya, wanda yake tsayawa takarar shugabancin Kamaru karkashin inuwarta.