RDC: Jagoran ′yan adawa ya koma gida | Labarai | DW | 20.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

RDC: Jagoran 'yan adawa ya koma gida

Jagoran 'yan adawar Kasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango Moïse Katumbi ya koma kasar shekaru uku bayan ya fice daga kasar bisa tuhumarsa da aikata laifi da tsohuwar gwamnatin Joseph Kabila ta yi a baya.

Moïse Katumbi da ke a matsayin tsohon gwamnan Katanga ya yi tozali da kasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango a yau din nan da inda ya sauka a filin saukar jiragen saman Lubumbashi, a yayin da yake fito wa daga Belgiyam kasar da ya shafe shekaru yana samun mafaka ta siyasa. 

Masu sharhi sun ce komawar dan adawar a gida ba ya rasa nasaba da samun wata kwarya-kwaryar fahimtar juna tsakanin sababin masu mulkin kasar ta Kwango da na bangaren 'yan adawa duba da yadda sabuwar gwamnatin ta soke hukuncin zaman gidan yari na shekaru uku da aka yanke wa Moïse Katumbi a baya. 

Sai dai a gaban dandazon magoya bayansa Moise Katumbi ya ce ya dawo kasar ne don kawo tasa gudumuwa da ci-gaban Kwango, ko da ya ke daga cikin wadanda suka je tarbon jagoran ba a ga wulgin Martin Fayulu ba, da ke a matsayin na kut da kut ga jagoran na 'yan adawa.