Rayuwa cikin fargaba a birnin Kabul | Siyasa | DW | 22.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rayuwa cikin fargaba a birnin Kabul

Tun bayan harin ta'addanci da ya kashe wani jami'in tsaro na Afganistan da Bajamushiya mai aikin agaji, tashar DW ta nemi jin ra'ayoyin jama'a kan rayuwar fargaba da tsoro a Kabul.

 

Amir, Nuri, Mujtaba da Isa sun shaidar da yadda rayuwa ta zame abun ban tsoro a Kabul. Akwai dandazon 'yan gudun hijirar a Kabul da aka iza keyarsu daga Jamus. Mummunan labarin harin da aka kai kungiyar ba da agaji ta kasar Sweden dai ya razana mutane.

Mazauna garin musamman 'yan wasu kasashe sun yi ta aikewa da sakonni gida domin tabbatar da 'yan uwa da abokan arziki cewar, suna cikin koshin lafiya. Hare-haren ta'addancin dai suna kama da juna, kama daga na birnin Kabul da Paris da Brussels da Nice sai kuma na Berlin. Kuma kawo yanzu babu cikakkun bayanai dangane dangane da irin wannan hari.

Sai dai bayan harin na ranar asabar a birnin Kabul, abubuwa sun fara fitowa fili. Domin 'yan kasashen waje aka nufa da harin. Kai tsaye akan ma'akatan agaji na kasa da kasa wadanda rayuwarsu ta ke da sarkakiya. Harin ya yi sanadiyyar rayuwakn jami'in tsaron Afganistan da ma'aikaciyar agajin Jamus, kana an sace jami'in agajin Finnland.


Wannan dai ba shi ne karo na farko da aka kai irin wannan hari kan baki a birnin na Kabul ba. Sai dai a yawancin lokuta abun ya kan ritsa ne da fararen hula 'yan kasar ta Afganistan. Kama daga farkon wannan shekara dai, an kai munanan hari makamancin wannan sau bakwai a birnin na Kabul, wanda ya yi sanadiyyar rayukan daururuwan mutane kana wasu sun jikkata. Mayakan Taliban ko na IS kan dauki nauyin harin.

Gundarin labarin dai shi ne babu tsaro a birnin na Kabul. Inda ya ke da tsaro a yau zai iya zama wurin da za'a kai hari gobe. Hakan na faruwa ne duk ta kasancewar dakarun Amurka , a yayin da takwararta ta NATO ke kokarin aikewa da karin sojoji zuwa kasar ta Afganistan.