Rayuka sun salwanta a Philippines | Labarai | DW | 09.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rayuka sun salwanta a Philippines

A ƙalla mutane 1,200 suka rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka jikkata a ƙasar a sakamakon mahaukaciyar gugwuwar nan ta Haiyan da ta afkawa ƙasar

Jami'an ceton gaggawa na can na kai-kawo babu kama hannun yaro, don isa tsakiyar ƙasar inda lamarin ya yi ƙamari. A hukumance dai gwamnati ta ce mutane 138 ne suka mutu, amma jami'an kiwon lafiya da masu ba da agaji sun ce suna da ƙiyasasin mutane sama dubu ɗaya waɗanda lamarin ya hallaka kawo yanzu.

An bayyana cewar sama da mutane dubu 750 ne guguwar ta tilastawa ƙauracewa gidajensu, inda hukumomi da jami'an tsaro da na ba da agaji ke ƙoƙarin kwantar wa da mutanen hankula, kan cewar za a ba su agajin gaggawa. Wani jami'i a hukumar kare afkuwar bala'oi ta Majalisar Ɗinkin Duniya Sebastian Rhodes Stampa, da ke cikin tawagar da ta isa ƙasar ta Philippines don ba da agajin gaggawa, ya ce mahaukaciyar guguwar ta ƙasar Philippines kusan iri ɗaya ce da annobar tsunami da yankin Asiya ya fuskanta a shekara ta 2004 da ta yi sanadiyyar mutuwar sama da mutane dubu 20.

Mawallafi : Usman Shehu Usman
Edita : Abdourahamane Hassane