Raya ranar raggwanci a Kwalambiya | Labarai | DW | 21.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Raya ranar raggwanci a Kwalambiya

Al'ummar birnin Itagui na Kwalambiya a jiya lahadi ta gudanar da bikin raya ranar da ta yi wa lakabin ranar raggwanci a wani mataki na yaki da damuwar da jama'a ke fama da ita a sakamakon aiki.

Al'ummar birnin Itagui na kasar Kwalambiya ta gudanar a jiya Lahadi da bikin raya ranar da ta yi wa lakabin "Ranar raggwanci" ta kasa inda a tsawon yinin jiya Lahadi jama'a maza da mata, yara da manya suka shimfida katifu da tabarmi a ko'ina a cikin birnin domin hutu a tsawon yinin ranar ba tare da yin wani aiki ba.

 Yau shekaru 32 kenan dai da al'ummar birnin na Itagui na Arewa maso Yammacin kasar da kuma ke kunshe da mutun dubu 200 ta kaddamar da wannan rana ta raggwanci a wani mataki na yaki da matsalar damuwa da ke addabar al'ummar birnin a sakamakon tsananin aiki. 

Al'ummar birnin Atagui, al'umma ce da ta yi fice wajen azama a fannin harakokin kasuwanci da kuma na kamfanoni.Wasu alkalumman bincike na shekara ta 2007 a kasar ta kwalambiya sun nunar da cewa kashi 24% na maza da 28% na mata na fama da matsalar damuwa a sakamakon tsananin aiki.