Rawar da Gaddafi ya taka a nahiyar Afirka | Siyasa | DW | 19.10.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rawar da Gaddafi ya taka a nahiyar Afirka

Gaddafi ya shafe shekaru 40 ya na taka muhimmiyar rawa a al'amuran siyaysa da tattalin arzikin Afrika.Har zuwa lokacin mutuwarsa, ya rika mafarkin samar da Taraiya ta Afrika da za ta kasance karkashin jagorancin sa.

SIRTE, LIBYAN ARAB JAMAHIRIYA: A delegate walking in a hallway of the Sirte Conference Centre observes a billboard with Libyan president Muammar Khadafi hosting the Fifth Ordinary Session of the Assembly of the African Union 03 July 2005. Preliminary and comity meetings are being held in this city 450 kilometers east of Tripoli in preparation to the two-day presidential summit expected 04 July. AFP PHOTO/CRIS BOURONCLE (Photo credit should read CRIS BOURONCLE/AFP/Getty Images)

Plakat Gaddafi AU Gupfel 2005

Muammar Gaddafi ya rika kiran kansa dan uwan duk masu juyin juya hali: Ya kuma rika kiran kansa sarkin sarakuna. To amma duk inda aka duba, za'a ga cewar Gaddafi ya kasance mutum ne mai fuskoki da dama. Ko da shike ga kasashen yamma Gaddafi shugaba ne mai mulkin kama karya, maras imani kuma mai son kansa, amma wace irin fuska Gaddafi ya mutu ya barwa kasashen Afrika? Fred Opolot, kakakin gwamnatin Uganda ya yabi dangantakar dake tsakanin kasar sa da Gaddafi.

"Gaddafi ya kasance kyakkyawan aboki ne ga kasar Uganda tsawon shekaru da dama. Gaddafi ya taka muhimiyar rawa a gwagwarmayar neman mulkin kan Uganda, kuma Gaddafi din zai sami wuri na musamman a tarihin kasar Uganda."

Ugandan President Yoweri Museveni (L) speaks with Libyan leader Moamer Kadhafi on the last day of the 15th African Union Summit in Kampala, on July 27, 2010, as 30 heads of state from the AU's 53 members gathered for three days amid unprecedented security in the Ugandan capital. AFP PHOTO/MAHMUD TURKIA (Photo credit should read MAHMUD TURKIA/AFP/Getty Images)

Uganda na cikin kasashen da Gaddafi ya zuba jari

Gaddafi mutum ne da aka rika marhabin da jarinsa a tattalin arzikin kasashen Afrika da dama. Ya giggina manyan hoter-hotel a nahiyar, tun daga Kenya har zuwa Ghana. Ya gina masana'antu a Liberia da Guiinea. Ya kuma bude gidajen sayar da jan fetur a Afrika ta gabas baki daya. To amma duk da haka, lokacin yakin Libya, kasashen na Afrika sun bi umurnin kudirin kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya, inda suka toshe dukkanin kudade da dukiyoyin da iyalin Gaddafi suka mallaka a cikin su. A yanzu kasashen na Afrika sun dage wannan takunkumi, kuma hukumar zuba jari ta Libya har yanzu tana nan, amma kudin da ta mallaka ya samu ne tun kafin zamanin da Libya ta shiga yaki.

Gaddafi ya kafa kanfanoni a kasashen Afirka da dama

A woman celebrates on the streets after casting her vote during the National Assembly election in Tripoli's Martyrs square July 7, 2012. Crowds of joyful Libyans, some with tears in their eyes, parted with the legacy of Muammar Gaddafi on Saturday as they voted in the first free national election in 60 years. REUTERS/Zohra Bensemra (LIBYA - Tags: ELECTIONS POLITICS)

Juyin juya hali ne ya yi awan gaba da mulkin Gaddafi

Ga kasashen Afrika da dama, mutuwar Gaddafi babbar asara ce ta fuskar tattalin arziki, kamar yadda wani mai sharhi na Afrika ta yamma, Sebastian Spio-Garbrah, wanda ma yace har yanzu wadannan kasashe ba su san abin da zai zama makomar hotel-hotel da kamfanoni da manyan gonakin da Gaddafi ya bude a cikinsu ba, musmaman saboda kasashen da dama har yanzu ba su yarda da take-taken sabuwar gwamnatin dake mulki a Libya ba. A lokacin yakin, jarin Libya ya kasance karkashin kulawar kasashen da jarin yake. A yanzu ko da shi ke an kafa sabuwar gwamnati a Tripoli, amma kasashen Afrika da dama sun ki mika wannan jari zuwa ga sabbin masu mulkin.

"Kasashen Afrika da dama ba sa farin ciki game da abin da zai zama makomar jarin Libya dake cikinsu, saboda haka ne da yawa daga cikin su har yanzu suka ki mika bangaren jarin na Libya zuwa ga sabin masu mulki acan. Ko da shi ke ta diplomasiya sun amince da sabuwar gwamnatin ta Libya, amma sun ki mika jarin kasar dake hannun su ga sabbin shugabanin."

Gaddafi ya zama uwa da makarbiya a kungiyar Tarayyar Afirka

FILE - In this March 8, 1977 file photo Cuban leader Fidel Castro and Moammar Gadhafi meet in Tripoli, Libya. As rebels swarmed into Tripoli late Sunday, Aug. 21, 2011, and Gadhafi's son and one-time heir apparent Seif al-Islam was arrested, Gadhafi's rule was all but over, even though some loyalists continued to resist. (AP Photo, File)

Tun ya na matashinsa ya dare kan kujerar mulkin Libya

A bayan jarin da Gaddafi ya zuba a Afrika na kudi, me kuma zai zama makomar jarinsa na siyasa a nahiyar. Me zai zama makomar mafarkinsa na Tarayyar nahiyar Afrika, musmaman ganin cewar shi ne ya matsa lambar ganin an kirkiro kungiyar AU? Ulf Engel masani kan al'amuran Afrika a jami'ar Leipzig ya ce neman kafa Tarayyar Afrika yanzu dai baya cikin lissafi, tun da ma shugabannin kasashen Afrika da yawa suna ganin Gaddafi ya wuce gona da iri a bukatunsa na neman shugabacin nahiyar baki daya. Ya ce Gaddafi ya zama shine wuka, shi ne nama a harkokin nahiyar Afirka ne saboda kudinsa.. Libya ita kadai take biyan kashi 15 cikin dari na kasafin kudin kungiyar AU, yadda kasar zata sami abokai ta kuma rika sayen kuri'u a duk lokacin da aka zo yanke wani kudiri. To amma kungiyar ta AU a yanzu tafi kuzari, ba tare da Muammar Gaddafi ba, inji Ulf Engel.

"A shawarwari da na sha yi da kungiyar AU, na ga alamar cewar yanzu kungiyar tafi sakin jikinta, saboda rashin mai da hankali ga manufofin da ake yinsu saboda neman suna da shiga kanun labarai kawai. Maimakon haka, yanzu kungiyar ta fi mai da hankali ga muhimman al'amura da yadda zata karfafa aiyukan kungiyoyinta daban daban."

Halin da kungiyar Au ta ke cikin bayan mutuwar gaddafi

epa03084101 A handout photograph provided by the South African Government Communication and Information System (GCIS) shows President Jacob Zuma (L) meeting with Republic of Congo-Brazzaville President, Denis Sassou-Nguessoa (R) during the 26th meeting of the NEPAD Heads of State and Government Orientation Committee (HSGOC) being held, Addis Ababa, Ethiopia, 29 January 2012. EPA/ELMOND JIYANE /GCIS / HANDOUT HANDOUT EDITORIAL USE ONLY/NO SALES

Afirka ta kudu na fada a ji a kungiyar Tarayyar Afirka

Shekara guda bayan Gaddafi, yanzu dai sabbin shugabanni ne suke fitowa kungiyar ta AU. A fannin siyasa, Afrika ta kudu ta na iya samun karin ikon fadi a ji a kungiyar, ganin cewar 'yar kasar, Nkosazama Dlamini Zuma itace yanzu sabuwar shugaban hukumar kungiyarta AU. Akwai kuma sabbin masu zuba jari dake bullowa. Sabuwar hedikwatar kungiyar AU a birnin Addis Ababa, wuri ne da aka gina shi bisa kudi dollar miliyan 200, kyauta daga kasar China.

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Mouhamadou Awal

Sauti da bidiyo akan labarin