Rasuwar Yar′adua | Labarai | DW | 06.05.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasuwar Yar'adua

A yau da rana za'a yi jana'izar marigayi shugaban Najeriya Alhaji Umaru Musa Yar'adua

default

Umaru Musa Yar'Adua

Allah ya yi wa shugaban Najeriya Alhaji Umaru Musa Yar'aduwa rasuwa. Kakakin gwamnatin ƙasar ne ya bada sanarwar a hukumance. Yar'aduwa mai shekaru 58 da haifuwa, ya daɗe yana jinya sakamakon cutar zuciya. Mataimakin shugaban ƙasar Goodluck Jonathan wanda ya kasance muƙaddashin shugaban ƙasa tun a watan Febrairu ya sanar da makoki na kwana bakwai. Jonathan dai zai kasance shugaba mai cikakken iko, inda za'a rantsar da shi nan da sa'o'i, kana zai ci gaba da riƙe shugabancin ƙasar har izuwa ƙarshen wa'adin Yar'aduwa cikin watan Mayun baɗi. Yar'adua dai ya yi gwamnan jahar ta Katsina na tsawon shekaru takwas kafin daga bisani ya ɗare kan shugabancin ƙasar a shekara ta 2007. An dai bayyana cewa aƙalla shekaru 10 ya yi yana fama da rashin lafiya, inda a cikin shekarun da ya yi na shugabancin ƙasar, sau biyu ana kawo shi nan ƙasar Jamus cikin gaggawa don ganin likita. Kafin daga bisani ya koma jinyarsa a ƙasar Saudi Arabiya. Izuwa yanzu dai shugabannin ƙasashen duniya sun fara aikawa da saƙonnin ta'aziya, ciki kuwa har da shugaban ƙasar Amirka Barack Obama wanda ya aika saƙon ta'aziya ga iyalan marigayi tsohon shugaban Najeriya. Obama ya ce yana tuna irin gaskiya da adalcin da marigayi Alhaji Umaru Musa Yar'adua ke da shi.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Muhammed Nasir Auwal